Almakura ya tsira daga zargi a Nasarawa | Labarai | DW | 05.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Almakura ya tsira daga zargi a Nasarawa

Kalilan daga cikin 'yan majalisa da ke zargin gwamnan Nasarawa ne suka hallara don kare matsayinsu. Saboda haka kwamitin bincike ya yi watsi da zarge-zargen nasu.

Kwamitin da aka kafa a Jihar Nasarawa ta tarayyar Najeriya domin ya binciki zarge- zargen da ake yi wa gwamna Tanko Almakura, ya yi fatali da zarge- zarge 16 da majalisar dokokin jihar ta yi masa. A wannan Talata da rana ne a garin Lafia, shugaban kwamitin Usman Shehu, ya yanke hukuncin kan zarge- zargen bayan da kwamitin ya yi zamansa.

'Yan majalisar Nasarawa na zargin Almakura da aikata laifuka daban-daban ciki kuwa har da wawushe dukiyar talakawa. Sai dai shida ne daga cikin 'yan majalisa 20, da suka nemi tsige gwamnan suka hallara gaban kwamitin tare da lauyoyinsu, inda suka ce ba su yarda da sahihancinsa ba. Don haka ba za su bayyana ba domin amsa tambayoyin kwamitin.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa daga Nasarawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe