Allah ya yi wa Ɗan-Maraya Jos rasuwa | Labarai | DW | 20.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Allah ya yi wa Ɗan-Maraya Jos rasuwa

Ɗan Maraya na daga cikin mawaƙan Hausa na Najeriya wanda waƙoƙinsa suka samu karɓuwa a duniya

A ranar Asabar(20-06-15) Ɗan Maraya ya rasu a garin Jos, bayan wata rashin lafiya da ya yi. Wani daga iyalen marigayin ya shaida wa wakilinmu na jihar Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi, cewar marigayi Ɗan maraya Jos, wanda aka haifa cikin shekarar 1946, ya kwanta rashin lafiya ne tsahon watanni biyu da suka gabata, inda kuma yau da rana rai ya yi halinsa.

Marigayi Ɗan Maraya ya kwashe shekaru da dama yana yin wakoƙi gargajiya na Hausa na gargaɗi kan zaman duniya da sauransu wadanda suka samu kaɓuwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta har ma a cikin sauran ƙasashen duniya. Yanzu haka dai ɗarurruwan jama'a masu ta'aziyya suna kan ziyartar garin Jos, don gabatar da ta'azziyarsu ga iyalen marigayin.