Alkallai sun kama alkalai a Burkina Faso | Labarai | DW | 26.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alkallai sun kama alkalai a Burkina Faso

Majalisar Alkalan shari'a ta kasar Burkina Faso ta aiwatar da hukunci kan wasu alkalan kasar guda hudu bayan da aka same su da laifin karbar na goro a hannun jama'a kafin su yi aikin da ya rataya a kansu.

Hukuncin dai ya kama daga kasheidi, zuwa rage karfin, yayin da wasu kan iya fuskantar kora daga bakin aiki. An dai samu wadannan alkalan da laifin karbar kudade wajen bayar da sakin talala, ko kuma abun da ya shafi karbar kudade a gaban shari'a, da kuma can wajen 'yan sanda masu bincike masu aiki hannu da hannu da mashara'antu. Binciken da majalisar alkalan kasar ta Burkina Faso ta yi, gabaki daya ya shafi alkalai 37, akwai kuma lawyoyi guda uku, da manyan  jami'an 'yan sanda hudu. Ofishin ministan shari'a na kasar ne dai ya shigar da kara a gaban majalisar alkalan wadda ta samu duba kundaye na alkalai 10 daga cikin wadanda ake zargin.