Aljeriya ta zama zakarar kwallon kafar nahiyar Afirka | Labarai | DW | 20.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aljeriya ta zama zakarar kwallon kafar nahiyar Afirka

Mahukuntan kasar Masar sun tsaurara matakan tsaro a filin wasan birnin Alkahira da kewaye, gabanin karawar tsakanin Senegal da Aljeriya.

Kasar Aljeriya ta lashe gasar kwallon kafa na kofin nahiyar Afirka bayan lallasa kasar Senegal da ci daya da nema a wasan karshe da kasashen biyu suka fafata a daren ranar Jmum'a a kasar Masar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Algeriya ke daukar kofin bayan da ta yi nasarar daga kofin a shekarar 1990.

Tun dai bayan kammala wasan dubban mago bayan 'yan wasan Aljeriya ciki da wajen kasar ke shagulgilan nuna murna kan nasarar lashe kofin karo na biyu bayan shekaru 29.

Sai dai kasashe kamar Faransa an jibge 'yan sanda sama da 2000 a wani mataki na hana barkewar rikici tsakanin magoya bayan Aljeriya da Senegal.

Tun gabanin wasan mahukuntan kasar Masar sun tsaurara matakan tsaro a filin wasan birnin Alkahira da kewaye, gabanin karawar tsakanin Senegal da Aljeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin