Aljeriya ta fara zaman makokin rasuwar hafsan sojinta Gaid Salah | Siyasa | DW | 23.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Aljeriya ta fara zaman makokin rasuwar hafsan sojinta Gaid Salah

Allah ya yi wa babban hafsan sojan kasar Aljeriya Janar Ahmed Gaid Salah rasuwa a ranar Litinin a sakamakon bugun zuciya. Ya yi ruwa da tsaki a harkokin tafiyar da kasar ta Aljeriya.

Janar Gaid Salah wanda ya rasu yana da shekaru 79, ya kasance jigo a harkokin mulkin kasar ta Aljeriya tun daga shekara ta 1962, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen tilasta wa Shugaba Abdelaziz Bouteflika yin murabus a watan Aprilun da ya gabata a bisa matsin lambar masu zanga-zangar neman sauyi.

Marigayi Janar Gaid Salah ya kuma kasance a sahun gaba na hukumar mulkin sojan da ta jagoranci kasar har ya zuwa zaben sabon shugaban kasa na ranar 12 ga wannan wata na Disemba wanda Abdelmajid Tebboune ya lashe.

Matasa a Aljeriya na zanga-zangar neman sauyi a tsarin tafiyar da kasar

Matasa a Aljeriya na zanga-zangar neman sauyi a tsarin tafiyar da kasar

Tuni dai sabon shugaban kasar ta Aljeriya ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar tare da nada Janar Said Chengriha mataimakin shugaban hafsan sojan kasar a matsayin sabon shugaban hafsan soja na wucin gadi na kasar.

Tun a wasu watanni da suka gabata matasa masu zanga-zanga a kasar ta Aljeriya ke yin kira da a samar da sabbin hukumomi na demukuradiyya da ba za a shigar da tsoffin jagororin kasar a ciki ba.

Sauti da bidiyo akan labarin