1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bouteflika ya amince ya sauka daga mulki

Ramatu Garba Baba
April 1, 2019

Ana sa ran a wannan Litinin ne, Shugaba Abdelaziz Bouteflika zai sanar da yin murabus daga gadon mulki a wani mataki na bayar da damar a aiwatar da dokar kundin tsarin mulki ta 102.

https://p.dw.com/p/3G030
Algerien, Algier:  Algerisches Militär fordert Absetzung von Präsident Bouteflika
Hoto: picture alliance/dpa

Tun a ranar Asabar da ta gabata ne, shugaban hafsan sojojin kasar ya ja hankalin fadar gwamnati mai mulki, da ta aiwatar da ayar dokar, wacce za ta kai ga nada shugaban majalisar dokokin a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar, matakin da ke zuwa jim kadan baya da Shugaba Bouteflika, ya sanar da nada sabin ministoci.

Ana ganin ajiye mulki da shugaban ke shirin yi,  zai iya kawo karshen dambarwar siyasar da kasar ta fada bayan da al'ummarta suka kwashi makonnin suna zanga-zangar adawa da mulkin Bouteflika na kusan shekaru ashirin.