Aljeriya: An tantance ′yan takara biyar | Labarai | DW | 03.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aljeriya: An tantance 'yan takara biyar

Hukumar zaben kasar Aljeriya ta sanar da sunayen mutane biyar kacal da za su fafata a takarar neman shugabancin kasar tun bayan boren da ya kawo karshen wa'adin Abdelaziz Bouteflika.

'Yan takara 23 ne suka mika takaradun nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasar Aljeriya bayan jerin zanga-zanagar da ya kawo karshen mulkin Abdelaziz Bouteflika..

Yanzu haka dai sunayen mutane biyar ne hukumar zaben kasar ta amince tare da mika wa majalisar zartaswar domin tabbatar da takararsu. A watan Afirilun shrekarar 2019 ne sojoji suka tilasta wa Shugaba Abdelaziz Bouteflika. yin murabus bayan shafe shekaru 20 a kan mulki.