Alhini game da rasuwar Margaret Thatcher | Labarai | DW | 08.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alhini game da rasuwar Margaret Thatcher

Shugabanin ƙasashen duniya na ci gaba da aika saƙonni ta'aziyya ga iyalan Margaret Thatcher da ma al'ummar Birtaniya baki ɗaya domin taya su alhinin rashin da suka yi

ARCHIV - Die ehemalige britische Premierministerin Margaret Thatcher am 6.10.1999 auf dem Jahreskongress der konservativen Partei in Blackpool. Der Falkland-Krieg zwischen Argentinien und Großbritannien war auch der Konflikt zweier schillernder Staatsleute: Die für ihre Unnachgiebigkeit berühmt gewordene Premierministerin Margaret Thatcher und Argentiniens Junta-Chef Galtieri. (zu Themenpaket Falkland) +++(c) dpa - Bildfunk+++

Margaret Thatcher

Ƙasashen Duniya na ci gaba da nuna alhini kan mutuwar Margaret Thatcher, tsohuwar Firaministar Kasar Birtaniya da ta rasu a safiyar yau.

Shugabannin Ƙasashe daban-daban sun bayyana Tatcher a matsayin gwarzuwa data taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Dimokraɗiyya a Duniya baki ɗaya.

A Jawabinsa daya gudanar a Birnin Madrid na kasar Spain gabanin taƙaita ziyarar sa a Kasar da kuma soke ziyarar aiki da ya shirya kaiwa Kasar Faransa, Firaministan Birtaniya David Cameron ya bayyana cewa tabbas sunyi gagarumin rashi.

"A matsayinta na mace ta farko da ta zamo Firaminista Margret Tatcher ta samun nasarori da dama, kuma ba wai kawai ta mulkin Kasarmu bane a'a tayi kokari wajen ceto Kasarmu, Za'a rinƙa tunawa da ita a matsayin wacce ta bautawa Ƙasarta yadda ya kamata kuma mutane za suyi koyi da ita kan hakan".

Shima Ministan harkokin wajen Ƙasar Jamus Guido Westerwelle, ya bayyan cewa mutuwar Margaret Tatcher ta shafi duniya baki daya.

"Mace ce da ba Kasar birtaniya ce kawai ta amfana da aiyukanta ba har Nahiyar Turai da ma Duniya baki daya. Ta kasance Fitacciyar "yar siyasa a Birtaniya da nahiyar Turai a karni na 20".

Shima Shugaban Amurka Barack Obama yace Amurkawa ba zasu manta da ita ba a matsayin abokiyar tagwaitakar Shugaban Amurka na wancan marigayi Ronald Reagan da ake ganin sun taka mhimmiyar rawa tare yayin yakin Cacar Baka da rusashshiyar Tarayyar Sobiet.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

I