1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahajjata da dama sun rasu a jifan shedan

Ahmed Salisu/Mahmud Yaya Azare/YBSeptember 24, 2015

Rahotanni daga Saudiyya na cewar Alhazai sama da 700 sun rasu sakamakon turmutsutsu da aka samu wajen zuwa jifan shaidan kana wasu da suka haura 800 sun jikkata.

https://p.dw.com/p/1GcTi
Saudi-Arabien Hadsch Massenpanik in Mina
Mahajjata cikin dimuwa wasu rai ya yi halinsaHoto: picture-alliance/AP Photo

Mahukunta a Saudia sun ce , maniyata sama da 700 ne suka rigamu gidan gaskiya, sakamakon turmitsitsin da aka samu a kan hanyarsu ta zuwa jifan shedan a Mina.

‘Yan kwana-kwana dai na ci gaba da kwashe gawarwaki da wadanda suka jikkata,a yayin da jami’an tsaro ke kokarin sauya akalar maniyatan subi wasu hanyoyin don samun daidadituwar lamura .

Ba a dai kai ga gama tantance wadanne kasashe abin yafi ritsawa dasu ba, amma dai ma’aikatar lafiya ta ce yawancinsu tsofaffi ne.

Saudi-Arabien Hadsch Massenpanik in Mina
Jami'ai na duba wadanda turmutsutsu ya ritsa da suHoto: picture-alliance/dpa/Saudi civil defence agency

Wata tsohuwa dake ci gaba da karbar magani a sibiti ta bayyana yadda abin ya faru;

Matsatsi ne sababi

“Muna kan hanyarmu ta zuwa Safa da Marwa, matsatsi ya yi matsatsi,sai kawai na ji nunfashina ya dauke.Daga nan ban san abin da ya faru ba. Na dai gammu haka zube a kasa jina jina.”

Saudi-Arabien Hadsch Massenpanik in Mina
Masu aikin agaji dauke da tsohoHoto: picture alliance/landov

Wani da ke kusa da inda hatsarin ya faru ya dora laifin hatsarin kan hukumar shirya aikin hajjin Saudiya da kuma wasu kamfanonin lura da maniyyata.

Askarawa sun taka rawa

“A ganina dalilai biyu ne suka jawo wannan hatsari, na farko kuskuren da hukumar shirya aikin Hajji ta yi, na mayar da hanyar tafiya kadai ta zama ta zuwa da dawowa, kana askarawa sukai ta tura mutane wai don su wuce. Sai kuma rashin bin ka‘ida da kamfanonin lura da maniyata, yadda suke saba lokuta da hanyoyin da aka tsara zasu dinga bi.”

To sai dai ministan lafiyar kasar ta Saudiyya ya musunta gazawar hukumar aikin hajji da jami‘an tsaro, yana mai dora alhakin faruwar hatsarin kan rashin bin ka‘idar maniyata.

Saudi Arabien Spezialpolizei Archiv 2013
'Yan sanda na SaudiyyaHoto: AFP/Getty Images/Fayez Nureldine

A farkon aikin Hajjin na bana dai, wanda mutane sama da miliyan biyu ke halarta, an fuskanci wani mummunan hatsari a lokacin da wata rumfa ta fada kan maniyata, wacce ta kai ga halakar fiye da mutane dari. Hatsarin da ya kai ga dakatar da kamfanin Bin Ladan da ya jima yana tarbar mahajjata, kana aka dakatar da jami‘ansa don gudanar da bincike.

A shekarun baya dai, an sha fuskantar turmutsitsi a wajen jifan shaidan din, amma bayan wasu gyare-gyare da mahukuntan na Saudiyya suka yi, an samu sauki a ‘yan shekarun nan.