Alfanun sake amfani da ledoji da robobi | Himma dai Matasa | DW | 21.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Alfanun sake amfani da ledoji da robobi

Ana iya sake sarrafa ledoji da rabobin da aka yi amfani da su, domin su taimaka wajen aiyukan yau da kullun na al'umma, wadanda suka hada har da gini.

Ledoji da robobin da aka yi amfani da su na ci gaba da gurbata muhalli a yawancin kasashen Duniya. To amma wani tsohon dan wasan kwallon kafa dan kasar Kamaru ya kafa masana'anta a yaonde da ke sarrafa wadannan robobi izuwa sabbin kira.

A yayinda yawancin 'yan kasar Kamru, ke ganin ledoji da sauran robobin da aka yi amfani da su a matsayin bola, shi kuwa Pierre Kamsouloum na matukar ganin darajar irin wadanna robobi da ake ya da su.Tare da hadin guiwar wasu 'yan kasuwa a kasar, Pierre ya kafa masana'antar juya robobi a kasar kamaru.

"A lokacin da muke kuruciyar da can a karkara,mukan tattara ledoji da robobi da akayi amfani da su sannan mu narkashi sannan da ga nan mu sarrafashi a matsayin tamola."

Kididdiga daga ma'aikatar kula da Muhalli a kasar Kamarun, ya nuna cewa ana kera robobi akalla ton 600,000 a duk shekara. Pierre ya ce masana'antar kera robobin zai kare muhalli sannan zai ba da damar samun aiyukan yi ga yawancin matasa da ke zaman kashe wando.

Bildergalerie Sportler aus Afrika - Roger Milla

Roger Milla, tsohon dan kwallon kafar Kamaru

Tsohon dan kwallon Kamaru ya ba da hadin-kai

Roger Milla wani dan asalin kasar Kamaru ne, wanda ya shahara a fagen wasan kwallon kafan kasar. Shi dai milla ya taka rawar gani a zamaninsa musamman a gasan cin kofin duniya ta 1990, a yanzu haka shi ke raya masana'antar ta samarda kuddaden gudanarda harkokinta.

"Idan ka kammala aikinka na wasan kwallon kafa, da akwai bukatar ka yi abin da zai taimaki al'ummarka. Shi ya sa na bullo da wannan dabarar dan taimakawa matasan kasar Kamaru"

A yanzu dai da dama daga cikin muhimman 'yan kasar Kamaru, na yabawa da irin wannan gagarumin namijin aiki na kafa masana'anta da ke juya tsoffin rabobi a kasar zuwa sarrafa ababe masu amfani.

"Na ga aikin ne ta wani shiri a telebijin, kuma hakika ya bani sha'awa sosai ta yadda na ke tunani a irin wannan abu ya kamata ya samu cikakken goyon baya da taimako."

A yanzu da kayayyakin gine-gine ke ci gaba da yin tsadar gaske musamman ma ginin zamani da ake yi da siminti, da alamar cewa al'ummumoi da dama na maraba da bullo da wannan farar dabarar, na yin gini da kayanda ake sarrafawa da tsoffin robobin.

A kullum dai tunani da mafarkin Roger Milla shi ne yadda zai fadada irin wadannan masana'antu izuwa sauran sassan kasar Kamaru dan ganin kowa ya amfana da ga gareshi.

Sauti da bidiyo akan labarin