Alassane Ouattara zai yi takara a zaɓen shugaban ƙasa | Labarai | DW | 25.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alassane Ouattara zai yi takara a zaɓen shugaban ƙasa

A Cote d'Ivoire ƙawancen jam'iyyun siyasar da ke yin mulki wato RHDP ya ƙaddamar da Alassane Ouattara a matsayin ɗan takarasa a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a cikin watan Oktoban da ke tafe.

Tsohon shugaban ƙasar na Cote d'Ivoire Henri Konan Bedie shugaban jam'iyyar PDCI babbar abokiyar ƙawance shugaban shi ne ya bayyana sanarwa.A lokacin wani babban taron na ƙawancen jam'iyyun siyasar da aka yi a Abidjan.

masu aiko da rahotannin sun ce ana sa ran cewar Alassane Ouattara ,zai iya samu nasara a zaɓen saboda rashin wani riƙaƙen ɗan takara bayan da aka tsare tsohon shugaban ƙasar na jam'iyyar FPI Laurent Gbagbo, a koutun ƙasa da ƙasa da ke hukuntan manyan laifuka wato ICC.Saboda zargin da ake yi masa na haddasa kisan ƙare dangi a zaɓen shekarun 2010.