Al′amurra na dagulewa kafin zabe a Guinea | Labarai | DW | 09.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'amurra na dagulewa kafin zabe a Guinea

Mutane biyu zuwa ukku sun halaka a birnin konakry a sakamakon fadan da ke ciga gaba da hada magoyan bayan bangaran masu milki da na 'yan adawar kasar

A kasar Guinea Konakry al'amurra na ci gaba da dagulewa musamman a babban birnin kasar wato Konakry a daidai lokacin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaben shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa mutane biyu zuwa ukku sun halaka a cikin tarzoma a birnin na Konakry a jiya Alhamis, a lokacin da magoya bayan madugun 'yan adawar kasar Cellou Dallein Diallo suka cinna wuta ga shagunan wasu matasa 'yan kabilar malinkes ta Shugaba Alpha Conde a babbar kasuwar Madina ta birnin na Konakry .

A yayin da a wannan Juma'a suma matasan wannan kabila ta Malinke dauke da kulake suka ja daga a gurare daban daban na birnin dama a bakin kasuwar ta Madina inda suka haramta wa 'yan kasuwa 'yan kabilar filani ta madugun 'yan adawa shiga kasuwar bayan da dama a daren jiya suka cinna wa shagunansu akalla 20 wuta.