1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amuran da ke ci wa mata tuwo a kwarya

March 8, 2013

Matan Afirka suna bin sahun takwarorinsu na duniya wajen ganin nemo hakkokin su. Sai dai a kasashe kamar côte d'Ivoire da Tarayyar Najeriya har yanzu suna fama da matsalolin fyade da kuma karancin kulawa yayin haihuwa..

https://p.dw.com/p/17taM
Hoto: picture alliance/dpa

A lokacin rikicin da ya biyo bayan zaben Côte d 'Ivoire a shekara ta 2010 , mata da yara sun fuskanci matsaloli na rayuwa ciki kuwa har da Kisa , da fyade da ma haifuwa kan tituna sanadiyar rashin asibitoci . saboda haka ne suka yi amfani da ranar mata ta duniya(8 ga watan Maris) wajen mika korafe korafen su ga hukumomin kasar. Umma ita ce Shugabar mata a unguwar Treiche Ville da ke Abidjan. Ta ce matsalolin matan Côte d'ivoire ke fuskanta ba su misaltuwa

" Matsalolin matan kasar Côte d' Ivoire na da yawa tun da maza da dama tun lokacin yaki suka rasa wuraren su na kasuwanci. Idan aka duba za a ga cewa maza da dama ne su ka dogara kan saye da sayarwa. A wasu wurare mata a yanzu haka su ne ke jan ragamar gida: 'Yan mata kuma da dama suna neman aikin yi don taya samarin su ke zaman kashe wando. Wasu lokutan mata ne ke biyan kudin wutar lantarki da ma abinci."

TBC Tuberkulose Frau Patientin Südafrika
Hoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Baban abin da Matan Côte d'Ivoire ke bukata shi ne zaman lafiya da hadin kan 'yan kasa . Saboda haka ne suka bukaci shugaba mai ci a yanzu Allasane Ouattara da ya dube su da idon rahama ta hanyar magance dimbim matsaloli da matan ke cin karo da su a rayuwarsu ta yau da kullum. Malama Hadjara ta bukaci a inganta halin rayuwar matan kasar baki daya.

"Mu matan kasar Côte d'Ivoire zaman lafiya mu ke bukata. Muna kira ga shugaban mu Allassane Ouattara da ya bar mantawa da mata, saboda ko lokacin zabe su ke fitowa kwai da kwarkwata su kada kuri'a. amma wata rana sai kaga 'yan siyassa sun manta da mata da yara , bayan a lokacin yaki mu mata da yara , mun fi kowa shan wahala."

TBC Tuberkulose Frau Patientin Südafrika
Hoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Burin matan Côte d'Ivoire

Wani abu da ke ci ma Mata Matassa tuwo a kwariya shi ne rashin samun mazajen aure: 'Yan mata na tarewa a gidajan samari ba tare da an daura musu aure ba. Saboda haka ne wata matashiya da ke aiki a wani shagon sayar da agogo, ta yi kira ga hukumomi da su samarwa matasa kafar samun kudin shiga o za su samu su aure su.

"Abin da mu ke fata shi ne, matasan mu su samu ayyukan yi don su aure mu , saboda ni gaskiya ina bukatar yin aure . Wanan rayuwa ta zaman haka ba ta burge ni. Ina so kuma Allah ya kawo zaman lafiya a kasar nan domin mun gaji da yaki "

Ita kuma Aicha Amadou mai shekaru 16 da haihuwa bukata ta yi a dora kasar Côte d'Ivoire kan alkiblar da zai tabbatar ma ta da zaman lafiya.

"Ba na fatan ganin yaki ya sake barkewa a kasa ta. Muna son zaman lafiya musumman ma mu 'yaya mata. A lokacin yakin da ya wuce na rasa iyaye na da yayyu na, yayin da wasu kuma sun rasa mazajen su da yara. Muna so shugaban mu Allassane Ouattara ya kara kokari wajen mayarda zaman Lafiya. Kuma muna fata yaki ya zama tarihi a kasar nan."

Dossier Afrika kochen Gericht Spezialität Essen
Hoto: Fotolia/Renate W.

Fatan matan kasar Côte d'Ivoire na farko shi ne zaman lafiya, yayin da na biyu kuma ya kasance farfado da tattalin arzikin kasar domin a samarwa al'uma ayyukan da za su ba su damar rike kan su. Ta wadannan hanyoyin ne za a iya rage kaifin talaucin da ke adabar matan an Côte d'Ivoire , wadanda su ka kasance kan gaba wajen dawainiya cikin gida.

Mawallafiya. Tilla Amadou
Edita: Mouhamadou Awal