Al′amura sun rincabe a Masar | Labarai | DW | 05.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'amura sun rincabe a Masar

Magoya bayan shugaban Masar Mohammed Mursi yanzu so suke su toshe wa masu adawa da shi hanyar garzayawa kotu.

Talaat Ibrahim Abdullah wanda Mursin ya nada a matsayin babban mai shari'a a watan Nuwamba ya ba da umarnin gudanar da bincike akan Mohammed al Baradai da ya taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel da tsohon shugaban kungiyar kasashen Larabwa, Amre Musa da kuma sauran shugabannin adawa. Kafafen da ke da alaka da aikin shari'a a birnin Alkahira sun ce an ba da wannan sammace ne bisa zargin da ake musu na cewa sun hanzuga jama'a ga yin juyin mulki da kuma leken asirin kasar Masar wa Isra'ila. Su dai magoya bayan shugaban da masu adawa da shi sun yi kira da a shiga zanga-zanga.

A jiya Talata kusan mutane dubu 10 suka yi tururuwa a gaban fadar shugaban da ke birnin Alkahira domin nuna rashin amincewa da dokar da ayyanar domin ba wa kansa karin iko da kuma sabon kundin tsarin mulki. Sai da kuma aka yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zangar-zagar. Mahukuntan kasar sun ba da sanarwar cewa masu zanga-zanga 35 da 'yan sanda 40 sun samu raunuka yayin zanga zangar. Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hilary Clinton ta yi kira ga 'yan kasar ta Masar da su koma kan teburin shawara domin samun mafita daga takaddamar da ake yi akan kundin tsarin mulkin.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar