Al′amura na sake rincabewa a Ukraine | Labarai | DW | 15.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'amura na sake rincabewa a Ukraine

Kakakin rundunar sojojin Ukraine ya ce 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha sun hallaka sojoji takwas tare kuma da raunata wasu 16.

Rahotanni sun nunar da cewa biyar daga cikin sojojin sun rasa rayukansu ne a yankin Luhansk na gabashin kasar sakamakon tashin da nakiya ta yi da su. Wannan dai shi ne adadi mafi yawa da aka bayyana na sojojin Ukraine din da suka hallaka tun bayan da bangarorin biyu da ke yakar juna suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Minsk. Yarjejeniyar ta birnin Minsk dai ta bukaci duka bangarorin biyu su janye manyan makamansu da ga filin daga, sai dai masu sanya idanu na kasa da kasa na bayar da rahotannin karya ka'idojin yarjejeniyar da ga baki dayan bangarorin. Sama da mutane 6,400 ne dai aka hakikance sun rasa rayukansu a yakin tun bayan barkewarsa a cikin watan Afirilun shekara ta 2014 kawo yanzu.