1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amari ya kara rincabewa a Siriya

June 7, 2012

Majalisar Dinkin duniya ta yi Allah wadai da kisan kiyashi da ake wa farar hula a Siriya, ta kuma in kira da a ba da taimako wajen yin aiki da shirin Kofi Annan

https://p.dw.com/p/15AKV
In this Wednesday, Feb. 22, 2012 citizen journalism image provided by the Local Coordination Committees in Syria and accessed on Thursday, Feb. 23, 2012, flames rise from a house from Syrian government shelling, at Baba Amr neighborhood in Homs province, Syria. A French photojournalist and a prominent American war correspondent working for a British newspaper were killed Wednesday as Syrian forces intensely shelled the opposition stronghold of Homs. (Foto:Local Coordination Committees in Syria/AP/dapd) THE ASSOCIATED PRESS IS UNABLE TO INDEPENDENTLY VERIFY THE AUTHENTICITY, CONTENT, LOCATION OR DATE OF THIS HANDOUT PHOTO
Hoto: dapd

Jami'an sa ido na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) a Siriya sun fuskanci luguden wuta a aikinsu na gudanar da bincike kan kisan kiyashin da ya afku a lardin Hama. Babban sakataren majalisar Ban Ki-Moon ya fada wa mashwartar majalisar da ke a birnin New York cewa an kai wa jamian hari ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kauyukan Al Kubeir da Maasaraf inda a cewar 'yan adawa dakarun gwamnati da 'yan tawaye suka kashe mutane da dama. Gabanin haka an samu rahotannin da ke nuni da cewa dakarun gwamnati sun dakatar da jami'an sa ido a lokacin da suke hanyar zuwa kauyuka. Babban sakataren na MDD ya ce babu halacci da ya rage wa shugasbancin Bashar al Assad. A yau ne kofi Annan ya gabatar da rahoto a gaban babban maswaratar MDD inda ya bayyana shirinsa na zaman Lafiya tamkar abin da ya ci tura yann mai cewa:

"Yau ya zamo wajibi in in yi magana tsakani da Allah in kuma tabbatar muku da cewa duk da cewa an amince da shirin mai kudurori shida, an kuma tura 'yan sa ido na MMD zuwa Siriya, to amma an kasa zartar da wannan shiri."

Kantomar kungiyar Tarayyar kan manufofin ketare Catherine Ashton ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake wa fara hula a kasar ta Siriya. Ashton ta kuma yi Allah wadai da yunkurin yin karan tsaye ga shirin samar da zaman lafiya mai kudurori shida da Kofi Annan ya gabatar. Tace lokaci ya yi da za a daidata kan daukar mataki na bai daya ba tare da bata lokaci ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman