Al´adun yan ƙabilar Dogon na ƙasar Mali | Zamantakewa | DW | 19.09.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Al´adun yan ƙabilar Dogon na ƙasar Mali

Ƙabilar Dogon a ƙasar Mali ta fara cenza al´adun ta a dalili da sauyin zamani da yaɗuwar addinin musulunci

default

Masu sauraro assalamu alaikum barka mu da warhaka, lale marhabin da sake saduwa da ku a wani saban shiri na taba ka lashe.

A yau shirin zai kai mu ƙasar Mali, inda za mu duba wasu daga al´adun yan ƙabilar Dogon da ke wannan kasa, wanda har yanzu su ka rike al´adunsu na iyaye da kakanni, duk da cewar da dama daga cikin su sun rundumi addinin musulunci.

Al´umar ƙasar Mali da ke yammacin Afrika kashi 70 cikin ɗari musulmi ne,sai kuma sauran suna biyar adini kristanci kokuma arnanci, kamar misali yan ƙabilar Dogon da ke rayuwa a gabacin wannan ƙasa, wanda har ya zuwa yanzu su ke ci gaba da biyyaya ga addinin su na gadin-gadin, tare da bautawa gummuka.

To saidai da dama daga cikin su sun musulunta, ko da yake akwai sauran tabo a gare su na biyaya da wani alan da ba Allah ba.

Ta la´akari da mahimmanci galgajiya da al´adu a rayuwar jama´a hukumar bada agaji ta kasar Jamus wato DED ta yanke shawara kebe wani wuri na mussamman a gabancin ƙasar ta Mali domin dawwamar da al´adun yan kaɓilar dogon, ta yadda ba za su ɓace ba.

Seydu Guindu na daya daga al´umomin wannan ƙabila ya kuma bada ƙarin haske, a game da wannanal´ada.

„A garin mu, idan wata matsala ta ƙarancin ruwan sama ta abku, mu na anfani da al´adun mu na galgajiya.

Ka ga waccen yar bukar ? wasu gumaka ne, a ciki ,wanda mu ke bautawa.

Saidai yanzu ta la´akari da ci gaban addinin musulunci, da dama sun yi watsi da wannan al´ada, amma duk da haka, idan al´ammura su ka yi zafi, ruwan sama su ka ɗauke, mutane kann hita ƙauyen gari, su roƙi ruwa wajen wannan gumaka.

Kuma kamin sun koma gida, har an kece da ruwan, suna shiga gidajen su cikin ruwa sharkap“.

A yankin Dogon lokaci zuwa lokaci, ana fuskantar ƙarancin ruwan sama. A sheakaru kimanin50 da su ka wuce akwai namomin daji da kado da dama, amma yanzu kusan duk sun ɓata ta la´akari da cenji yanayi.

Wasu mazauna yankin, na dangata wannan cenji, da yin watsi da ala´dun su da kuma addinin su na gargajiya kamar yadda wani daya su ke bayanawa.

„Yau da shekaru fiye da 100 mutane garin Oreletane su ka watsar da gumakan su, da gidajen su na gargajiya, tun bayan wannan lokaci su ke fuskantar bila´o´i iri –iri, mussamman ma, su na samun fari akai akai , wato ba su samin damana mai albarka, duk inda su ka je, sai a ce da su, muddun ba su maido da gumakan su ba, kuma su ka koma a gidajen su na gado, ba za su taɓa samin zaman lahia da kwanciyar hankali ba“.

Tun shekara ta 1999 hukumar bada agaji ta ƙasar Jamus wato DED ta girka wata cibiyar al´adu a yankin yan ƙabilar Dogon na ƙasar Mali , hakan ya taimaka matuƙa gayya, wajen tallata al´adun wannan ƙabila a ƙasashen dunia

Wannan cibiya ta ƙunshi gidan kallo da al´adu, yan ƙabilar Dogon.

Saboda mahimmancin wannan al´adu, hukumar kulla da ilimi da al´adu ta Majalisar Ɗinkin Dunia wato Unesco ta ƙaddamar da wannan ƙabila a matsayin wani yankin mallakar ƙasa da ƙasa.

A shekaru 50 da su ka wuce, yan ƙabilar Dogon na gudanar da rayuwar su, a cikin tsaunukan Bandiagara keɓe da sauran al´ummomin dunia.

Amma daga bisani sun karɓi addinin musulunci su ka kuma fita daga cikin tsanuka domin girka garuruwa da massalatai.

Amadu Intine na ɗaya daga masu garuruwan da yan ƙabilar dogon ke rayuwa a cikin su a yanzu, ya na mai tsokaci kamar haka:

„Ibadar mu ta gargajiya, ba za ta tafi ba, tare da addinin muslunci ba, domin musulunci ya haramta bautawa wani allan da ba Allah ba.

Mafi yawan mu, mun yi watsi da wannan shirka, amma har yanzu akwai masu ra´ayin riƙau, wanda ke bautama gumaka, daga cikin su har da ma wanda su ka shiga musuluncin“.

Shekaru aru –aru, yan ƙabilar Dogon su ka share su na rayuwa irin ta su keɓe da duk hayaniya ko mu´amila da sauran jama´a.

Addinin musulicin ya shiga ƙasar Mali tun ƙarni na 12, amma bai issa ga yan Dogon ba in banda daga bisanin nan.

A hayin yanzu rayuwa ta fara cenzawa kwatata a wannan yanki, mussamman a dalili da mahimman abubuwa guda 3, na farko su cenji yanayin mahhali, na 2 karbar addinin musulunci sai kuma na 3 yankin ya fara buɗuwa ga sauran sassa na dunia ta la´akari da yan yawan buɗa ido, daga ƙasashen dunia, da ke zuwa ganin ƙwam a kai a kai.

A cewar mai gari Amadu Intime, zuwan turawa yan yawan bude ido, ba ƙaramin alheri bane, ga wannan yanki, ta la´akari da kuɗaɗen shiga da ya ke samu.

Babban ƙalubalen da a halin yanzu ke gaban yan ƙabilar Dogon shine na bada haɗin kai, ga neman ilimi, domin kuwa duk da cenjin da aka samu, jama´ar yankin na tattare da duhun jahilci.

 • Kwanan wata 19.09.2007
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvSi
 • Kwanan wata 19.09.2007
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvSi