Al-uman ƙasar Georgia sun gudanar da zanga zanga. | Labarai | DW | 13.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-uman ƙasar Georgia sun gudanar da zanga zanga.

ɗaruruwan dubban magoya bayan jam’iyun adawa sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin Georgia, don nuna ƙin amincewarsu game da sakamakon zaben shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 5 ga watan janairu. Jam’iyun adawa, sun ce maguɗi da rashin adalci ya sa aka baiwa shugaba Saakashvili mai samun goyan baya daga Amirka nasarar lashe zaben don yin tazarce.

Masu zanga-zangan sun yi maci a kann titunan Tiblis, inda suka yi kira da a sake ƙidayar kuri’un. Sakamakon zaben da aka bayyana ɗazunnan, ya baiwa shugaba Saakashvilli kashi 53 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa, a yayin da shugaban adawa Levan Gachechiladze ya tashi da kashi 25 cikin dari.