1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Sisi ya zama shugaban Masar na takwas

June 8, 2014

An rantsar da tsohon hafsan soji Abdel Fattah al-Sisi a matsayin sabon shugaban Masar a harabar kotun tsarin mulkin kasar, tare da tsaurara matakan tsaro.

https://p.dw.com/p/1CESb
Ägypten Präsident Abdel-Fattah al-Sisi Vereidigung 08.06.2014 QUALITÄT
Hoto: Reuters

A wannan lahadin ce aka gudanar da bukin rantsar da Al-Sisi a matsayin shugaban masar na shekaru hudu masu gabatowa.

Daga bisani ne shugaba Mahmud Abbas da sarakunan larabawa daga yankin Gulf da wasu shugabannin Afrika, za su halarci liyafar murna a fadar shugaban kasa ta Ittihadiya, a birnin Alkahira.

Al-Sisi dai ya lashe kashi 96.9 na zaben shugaban kasa da ya gudana a ranakkun 26-28 na watan Mayu. Zaben da ya gudana kusan shekara guda bayan ya cimma nasarar kifar da mulkin Mohammed Mursi na jam'yyar 'yan uwa musulmi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu