1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Sisi ya nuna alamun tsayawa takara

March 4, 2014

Shugaban rundunar Sojin Masar Field Marshal Abdel Fattah al-Sisi ya nuna sha'awarsa ta tsaya takarar shugaban kasar wanda ke tafe nan ba da dadewa ba.

https://p.dw.com/p/1BJRF
Shugaban rundunar Sojin Masar Field Marshal Abdel Fattah al-SisiHoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin dillancin labaran Masar na Mena ya rawaito Al-Sisi na cewar ba zai iya yin watsi da kiraye-kirayen da galibin al'ummar kasar ke yi na ya shiga takarar shugaban cin Masar din ba.

Al-Sisi ya kara da cewar nan gaba kadan zai bada cikakken tabbaci dangane da batun tsayawarsa takarar shugaban kasar ta Masar wadda ke kan gaba wajen yawan al'umma a kasasashen larabawa.

Da dama dai na ganin cewar Al-Sisi zai iya lashe zaben muddin ya tsaya takara duba da irin goyon da ya ke samu daga sojin kasar da wasu fitattun 'yan siyasa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh