Al-Shebab ta kashe wani ɗan Faransa | Labarai | DW | 12.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shebab ta kashe wani ɗan Faransa

Masu kishin addini na al-Shabab sun kashe Denis Allex wani jami'in hukumar leƙen asiri na Faransa wanda suka yin garkuwa da shi tun shekaru ukun da suka wuce.

Wata tawagar dakarun ta sojojin ƙundubala na ƙasar Faransa ta kasa samun nasarar ceto wani jami'in ƙasar, wanda ƙungiyar yan 'tawaye ta Al Shabab na ƙasar Somaliya ta ke yin garkuwa da shi tun a cikin watan Yuli na shekara ta 2009.

A cikin wata sanarwa da ofishin ministan tsaro na Faransa ta fitar ,ta nunar da cewa rundunar ta dakarun hukumar leken siri ta DGSE ta kai samamen ne a cibiyar 'yan tawayen domin kuɓUtar da Denis Allex wani jami'in ƙungiyar da yan' tawayen suke tsare da shi kusan shekaru ukku. Jean Yve Le Drian wanda shi ne ministan tsaro na Faransa ya yi tsokaci akan wannan batu

''An gwabza ƙazamin faɗa wanda sa'ilin da ake yin wutar 'yan tawaye suka bindige Allex , sannan wasu sojojin Faransa guda ya mutu , wani ɗaya kuma ya yi ɓatan dabo. Hakazalika an kashe 'yan tawayen ƙungiar Al-Shabab guda 17. Sai dai Ƙungiyar ta ta musunta mutuwar jami'in wanda ta ce ya na a raye.

Mallafi :Abdourahamane Hassane
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe