Al-Shabab ta kaiwa shugaban Somaliya hari | Labarai | DW | 03.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabab ta kaiwa shugaban Somaliya hari

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mahmud ya tsallake rijiya da baya bayan wani hari da kungiyar nan ta al-Shabab da ke da alaka da al-Qaida ta kaiwa jerin gwanon motocinsa.

Somali government soldiers patrol the scene of an explosion in the capital of Mogadishu September 12, 2012. Somalia's al Shabaab rebels carried out a bomb attack on Wednesday that targeted a Mogadishu hotel where the president and Kenya's visiting foreign minister were holding a news conference, the group said. REUTERS/Omar Faruk (SOMALIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS SOCIETY)

Somalia Mogadischu Anschlag auf den neuen Präsidenten

Hukumomin Somaliya sun ce shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmud ya tsira da ransa da lafiya bayan wani da hari da ya rutsa da jerin gwanon motocinsa lokacin da ya ke kan hayar zuwa wani kauye da ke kudu da Mogadishu, fadar gwamantin kasar.

An dai yi wa jerin gwanon motocin shugaban kasar kofar rago ne inda aka harba rokoki kan motocinsa sai dai guda daga cikin manyan jami'in sojin kasar Mohamed Qorey ya ce babu wanda ya jikkata a harin, hasalima tawagar shugaban kasar ta karasa inda ta nufa don gudanar da wani taro.

Shi ma dai Nasir Abdurahman wanda harin ya auku kan idonsa ya ce bisa ga abinda ya gani, shugaba Mahmud bai jikkata ba bayan da aka kai harin.

Kungiyar al-Shabbab da ke gwagwarmaya da makamai a kasar ta Somaliya ta ce ita ce ta kai harin inda kakakinta Abdulaziz Abu Musab ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar sun farwa shugaban ne a yankin Buffow da ke daura da kauyen Merka mai tazarar kilomita dari daga Mogadishu, wanda ke zama guda daga cikin yankunan da a baya al-Shabab din ke iko da shi.

Tuni dai kasashen duniya wanda ke goyon bayan shugaba Hassan Sheikh Mahmud suka yi Allah wadai da harin.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahman Hassane