Al Shabaab ta kwace gari a Somaliya | Labarai | DW | 04.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al Shabaab ta kwace gari a Somaliya

Mayakan Al Shabaab sun karbe garin Leego da ke a kudancin kasar Somaliya, jim kadan bayan barin garin da sojojin tabbatar da zaman lafiya suka yi.

Garin mai nisan mil 80 a yankin arewa maso yammacin Mogadishu babban birnin Somaliyar, yanki ne da 'yan bindigar suka kashe akalla mutane 12 a makon da ya gabata. Wani mazaunin garin Farah Ahmed, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar da sanyin safiyar yau juma'a ne dai dakarun tsaron na zaman lafiya suka bar garin da lamarin ya faru.

Yanzu dai yankin na hannun Sheikh Abdiasis Abu Musab da ke jigon bangaren na Al Shabaab a wajen a yanzu.