Al Shabaab ta kashe mutane a Somaliya | Labarai | DW | 23.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al Shabaab ta kashe mutane a Somaliya

Rahotanni daga Somaliya na cewa wasu manyan fashe-fashe da suka auku da yammacin wannan Juma'a, sun halaka rayukan mutum fararen hula da kuma wasu jami'an tsaron tsaro na kasar.

Alkaluman da ke fitowa daga Somaliya na cewa wasu manyan fashe-fashe da suka auku da yammacin wannan Juma'a, sun halaka rayukan mutum 22 ciki har da jami'an tsaro. Fashewar farko ta tashi ne a kusa da wani Otel yayin da ta biyu ta tashi kusa da fadar shugaban kasa dukkaninsu da ke Mogadishu babban birnin kasar. Shaidu sun ce gabanin tashin nakiyoyin, sai da aka yi ta musayar wuta tsakanin maharan da jami'an tsaro.

Tuni kuwa kungiyar Al Shabaab ta dauki alhakin hare-haren, kungiyar da ta yi kaurin suna wajen kaddamar da munanan hare-hare kan ma'aikatun gwamnati da kuma wuraren da jama'a ke haduwa. Cikin watan Oktobar bara ma dai kungiyar ta kashe sama da rayuka 500 a birnin na Mogadishu, a wani harin da ta yi amfani da babbar motar daukar kaya shake da nakiyoyi.