1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta kai wani sabon hari a Somaliya

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 18, 2015

Kungiyyar 'yan tada kayar baya ta Al-Shabaab ta sake kwace wani gari a Somaliya daga hannun dakarun wanzar da zaman lafiya na Afirka da ke kasar.

https://p.dw.com/p/1GYNp
Al-Shabaab Kämpfer in Mogadishu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Kungiyar dai ta kwace akalla garuruwa uku a Kudanci da kuma tsakiyar Somaliya. Ko da a cikin watan da ya gabata ma kungiyar ta kai wani hari a sansanin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Afirka da ke yankin Janale tare da hallaka sojojin Uganda akalla 12.

A jiya Alhamis kungiyar ta samu nasarar kwace garin na Janale da ke da nisan kimanin kilomita 90 da kudancin Mogadishu babban birnin kasar. Tuni dai jami'an tsaron Somaliya da kungiyar ta Al-shabaab suka tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai gwamnatin Somaliyan ta yi watsi da nasarar da al-shabaab din ke samu ta na mai cewa garuruwan da ta sake kwacewar ba wasu masu muhimmanci bane.