Al-Shabaab ta halaka rayuka a Somaliya | Labarai | DW | 02.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabaab ta halaka rayuka a Somaliya

Wani harin kunar bakin wake ya halaka wasu mutane ciki har da kananan yara a wani hari a wannan Lahadi a Somaliya.

Hukumomin kasar sun ce maharin ya tarwatsa kansa ne cikin wata motar da ke shake da nakiyoyi, a wani shingen binciken ababen hawa a gundumar Howlwadag da ke wajen birnin.

Wasu sojoji masu binciken su uku na daga cikin wadanda hari ya halaka, a cewar mai magana da yawun magajin garin Mogadishu, Salah Hassan Omar .

Akwai ma wasu mutum 14 da suka jikkata ciki har da wasu kananan yara shida da yanayinsu ke da muni.

Galibin wadanda abin ya shafa dai sun fito ne daga makarantar Islamiyya, ana kuma fargabar samun karuwar wadanda za su iya mutuwa.

Kungiyar al-Shabaab dai ta dauki alhakin wannan hari.