Al Jazeera ta nuna wani saban faifen Videon Ussama ben Laden | Labarai | DW | 23.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al Jazeera ta nuna wani saban faifen Videon Ussama ben Laden

Gidan talbajan na Aljazeera, ya watsa wani saban faifen Video, mai ɗauke da jawabin Ussama ben Laden shugaban ƙungiyar Alqa´ida da Amurika ke nema ruwa jallo.

A cikin wannan jawabi Ussama Ben Laden yayi huruci a game zanen ɓatancin da da aka yi wa manzan rahama, a kawanakin da su ka gabata, da kuma yaƙe-yaƙe a ƙasashen Irak da Sudan, da kuma halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Ussama Ben Laden, ya danganta dukkan wannan ayyuka da mumunar aniyar Amurika da Turai, ta yaƙi da addinin Allah.

Hukunci da ƙasashen yamaci su ka yanke na mayar da gwamnatin Hamas saniyar ware , da rikicin da su ka kunna a ƙasar Irak, da Sudan, da sauran wurare daban-daban na duniar musulmi,na nuni ƙarara, niyar wannan ƙasashe ta yaƙar addinin musulunci.

A game da haka, Ussama ben Laden,yayi kira ga musulmin dunia, zuwa haɗin kai, domin maiyar wa kura aniyar ta, ta hanyar yaƙar maƙiya addinin Allah.