Al Abadi ya baiyana nassara kan IS a Mosul | Labarai | DW | 10.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al Abadi ya baiyana nassara kan IS a Mosul

Firaministan Iraqi Haidar al-Abadi, a hukumance ya baiyana samun nasara akan yan IS a birnin Mosul.

Wannan dai na zama koma baya mafi girma da IS din ta samu tun bayan da ta ayyana birnin na Mosul a matsayin Daular ta.

Tun da farko a yau Firayim Ministan Irakin Haider al-Abadi ya gana da shugabannin al'ummar Kiristoci marasa rinjaye a Mosul domin tattauna makomar arewacin birnin bayan nasarar kabbabe yan kungiyar IS. 

Al Abadi wanda ya isa birnin na Mosul a jiya Lahadi ya kuma gana da kwamandojin sojin inda ya taya su murna kan jaruntakar da suka nuna a yakin.

“Yace muna kan matakin karshe na murkushe Daesh baki daya. An riga an yi musu kawanya kuma an basu zabi su yi saranda ko kuma a kashe su. Wannan shine abin da muka yi. Yawancin yan  Daesh a Mosul an hallaka su”.