al-Abadi: Ina so in sake jagorantar Iraki
July 13, 2019Tsohon firaministan Iraki Haidar al-Abadi ya ce a shirye yake ya sake zawarcin kujerar mulki sakamakon kalubalen da kasar ke fuskanta musamman a fannin cin hanci da rashawa da kuma rikicin addini. Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da 'yan Iraki ke bayyana rashin jin dadinsu dangane da salon mulkin gwamnati da ke ci yanzu, inda katsewar wutar lantarki ke neman zama ruwan dare duk da tsananin zafi da ake fama da shi.
Al-Abadi na rubanya tarurruka da shugabannin dabam-dabam ciki har da Ayatullah Ali Sistani, wanda goyon bayansa ke da mahimmanci wajen samun mukamin firaministan kasar Iraki. Shi dai Haidar al-Abadi ya kasance firaminista dan Shi'a daya tilo da aka yi wa tarba ta arziki a lardunan 'yan Sunni da yaki ya daidaita bayan da ya bayyana nasarar murkushe kungiyar IS a karshen shekara ta 2017. sai dai Firaministan da ke ci yanzu Adel Abdel Mahdiya karyata jita-jitar da ake yayatawa game da aniyarsa ta yin murabus.