Alƙalai na yajin aiki a Kwango | Labarai | DW | 04.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alƙalai na yajin aiki a Kwango

Daruruwan alƙalai masu sharia a ƙasar sun shiga yajin aikin na se baba ta gani tun daga jiya Litinin a Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango sakamakon rashin samun albashi.

Shabani Watenda alƙali a birnin Kinsasha ya bayyana cewar sun shiga yajin aikin ne saboda jan kunne ga gwamnatin ƙasar ta riƙa cika alƙawuran da ta yi.

Ya ce a shekarar 2011 shugaban ƙasar da kansa ya bayyana cewar mafi ƙanƙantar alƙali, ze riƙa karɓar albashi dala dubu da ɗari shida amma har yanzu babu abin da suka gani . Ya kara da cewar mafi ƙanƙantar alƙali a yanzu a ƙasar na karɓar kamar dalar Amirka 650 ga shi kuma ba sa cin moriyar shirin inshorar lafiya.

A dai watan Satimba na shekarar 2011 ne shugaba Joseph Kabila a lokacin kamfen ɗinsa ya bayyana cewar an ƙara wa alƙalan kasar albashi daga dala 724 a shekarar 2008 zuwa dala 1,600 a 2011.

Shi dai fannin shariar wannan kasa na shan fama da suka daga masu sanya idanu na cikin gida da ma na Ƙasa da Ƙasa bisa zargin sanya siyasa a harkokinsa dama rashin inganci cikin sha'anin shari'a.