Alƙa′ida na ƙara ƙarfi a Iraƙi | Labarai | DW | 05.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alƙa'ida na ƙara ƙarfi a Iraƙi

Mayaƙa da ke adawa da gwamnatin Iraƙi sun zafafa yaƙin da suke yi da gwamnati, kawo yanzu mutane da yawa suka mutu

'Yan sandan Iraƙi sun faɗi cewa garin Fallujah ya fada hannun ƙungiyar Alƙa'ida. Mayaƙan na Alƙa'ida sun fara kai farmaki ne a birnin Fallujah da Ramadi a jihar Anbar, tun ranar Litinin da ta gabata. Tarzumar ta fara yin ƙamari ne, bayan da dakarun gwamnati suka rusa wani sansanin da 'yan kungiyar ta Alƙa'ida suka kafa. Inda suke yin boren cewa ana danne musu haƙƙi ƙarƙashin gwamnatin da 'yan Shi'a suka fi rinjaye. Wannan ƙungiyar da ke ƙiran kanta, "Dakarun wanzar da Musulunci a Iraƙi" ita ce ta fi ƙarfi a cikin 'yan ta'adda da ke kiran kansu 'yan tawayen Siriya, abin da kuma ya sa ake ganin ƙungiyar na daɗa yin ƙarfi a yankin. Ko da a jiya Sabar, ƙungiyar ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin harin bam da aka kai a ƙasar Lebanon a wannan mako.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu