Akwai hadarin barkewar rikici a tsibirin Fiji | Labarai | DW | 02.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akwai hadarin barkewar rikici a tsibirin Fiji

Hafsan sojin tsibirin Fiji Commodore Voreqe Baini-Marama ya yi gargadin cewa tsibirin dake can cikin tekun Pasifik ka iya tsunduma cikin wani mummunan tashin hankali idan gwamnati ba ta janye wasu dokoki da ta ke kafawa ko ta yi murabus ba. Duk da haka hafsan sojin ya musanta rahotannin dake zargin sojin kasar da shirye shiryen kifar da gwamnatin FM Laisenia Qarase. Tuni dai FM ya yi watsi da bukatun Baini-Marama na soke wata sabuwar doka wadda ta tanadi yin afuwa ga ´yan kishin kasa na Fiji wadanda suka yi juyin mulki a watan mayun shekara ta 2000. a halin da ake ciki kasashen Australiya da New Zealand sun kammala shirye shiryen kwashe dubban ´yan kasashen su daga Fiji idan wani rikici ya barke.