Akalla mutane 14 aka kashe a wani hari da aka kai a Beirut | Labarai | DW | 15.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akalla mutane 14 aka kashe a wani hari da aka kai a Beirut

Sai dai wasu rahotanni sun ce yawan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hari da aka kai a kudancin babban birnin na Lebanon ya kai mutum 20.

Wani harin bam da aka kai da mota a birnin Beirut na kasar Lebanon yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 14 sannan wasu 200 sun jikkata. Sai dai wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce yawan wadanda suka rasu a harin da aka kai a kudancin birnin dake zama cibiyar kungiyar Hezbollah ya kai mutum 20. 'Yan sanda da ma'aikatan agaji na kungiyar Red Cross sun fada wa kamfanin dillancin labarun Jamus na DPA cewa daga cikin wadanda suka samu raunukan na kwance rai hannun Allah a asibiti. Shugaban Red Cross a Lebanon George Kattaneh ya kara da cewa har yanzu akwai mutane da suka makale cikin gidajensu suna jiran a kai musu dauki. Wata kungiya mai kiran kanta Baradan Nana Aisha, uwar Muminai, wadda kawo yanzu ba a santa ba, ta dauki alhakin kai harin, tana mai bayyana shi da sako na biyu ga shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da kungiyarsa. A ranar 9 ga watan Yuli mutane 53 sun rasu a wani hari da aka kai a birnin na Beirut.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman