Akalla mutane 10 sun mutu a Iran | Labarai | DW | 01.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akalla mutane 10 sun mutu a Iran

Kafar talabijin na kasar ta ce an tabbatar da mutuwar mutane 10, bayan barkewar zanga-zanga mai tsananin da aka faro tun kwanaki hudu, inda suke adawa da salon shugabancin shugaban Hassan Rowhani.

'Yan sanda sun kame sama da mutane 100 a yayin zanga-zangar, sai dai ana fargabar yiwar fito na fito tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro bayan da wasu ke kiran a cigaba da gudanar da gangamin.

A jawabinsa na farko ta kafar talabijin ga al'ummar kasar tun bayan fara zanga-zangar, shugaban Hassan Rowhani ya ce 'yan kasar na da 'yancin sukar lamarin gwamnati, amma akwai bukatar su yi a hankali don gujewa saba doka.

"Mutane na da cikakken 'yancin sukar gwamnati, amma zanga-zanga ya sha bamban da tashin hankali. Wajibi mu mutunta tsari da dokoki na kare ra'ayin 'yan kasa. Sai dai ba za mu amince da marawa masu ra'ayin juyin juya hali su samu gindin zama ba, dole mu nuna damuwa kan kare rayukan al'ummar kasa."