Aikin Hajji: ′Yan Iran sun isa Saudiyya | Labarai | DW | 29.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin Hajji: 'Yan Iran sun isa Saudiyya

Dubban 'yan Iran sun shiga kasa mai tsarki da nufin sauke farali a aikin hajjin bana daidai lokacin da Riyadh da Tehran ke kokari wajen jingine rikicin diflomasiyyarsu.

Hukumomi Saudiyya suka ce kimanin alhazan Iran dubu 86 ne suka isa kasar don yin aikin hajjin tare da miliyoyin mahajatta da suka fito daga sassan duniya daban-daban. Al'ummar Iran da dama dai sun bayyana jin dadinsu game da wannan cigaban da aka samu inda da dama ke cewar dama bai kamata rikicin diflomasiyya ya shafi harkoki na addini ba. A shekarar da ta gabata dai 'yan Iran din ba su samu sukunin zuwa yin aikin hajji ba sakamakon rashin jituwa tsakanin mahukuntan Tehran da na Riyadh da kuma gaza amincewa da bangarorin biyu suka yi kan wasu tsare-tsare na aikin hajji.