Aikin ceto a inda kasa ta zaftare a Indonisiya | Labarai | DW | 14.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin ceto a inda kasa ta zaftare a Indonisiya

Masu aikin ceto sun fara amfani da manyan motoci wajen yashe lakar da ke kan hanyar zuwa Java a tsakiyar Indonisiya inda zaftarewar kasar ta hallaka mutane da dama.

Hukumomi yanzu haka sun ce an kwashe mutane 577 daga wajen da abinda ya faru zuwa tudun mun tsira ya yin da aka cigaba da neman mutane 72 da suka bace bayan aukuwar ibtila'in.

Masu aiko da rahotanni suka ce gabannin fara gyara hanyar shiga kauyen na Java da ke tsakiyar kasar, an ceto daruruwan mutane inda aka yi amfani da hannu da fartanyoyi wajen tono jama'a daga baraguzan da suka rufe su.

An dai alakata faruwar lamarin ne da ruwan sama da aka yi ta yi kamar da bakin kwaryar ranar Juma'ar da ta gabata kana yankewar haryar shiga yankin ta takara ta'azzara lamarin.