AI ta ce Shell na karya kan malalar mai | Labarai | DW | 07.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AI ta ce Shell na karya kan malalar mai

Amnesty International ta zargi kanfanin Shell da ke hako danyen mai a yankin Niger-Delta na Nijeriya da rashin fadan gaskiya game da malalar mai domin kauce ma biyan diyya.

Kungiyar Amnesty International ta zargi kanfanin Shell da ke hakar danyen mai da shaftara karya domin kare kanta daga matsalar malalar danyan mai da kuma gurbatar muhalli da ake fuskanta a yankin Niger-Delta na Tarayyar Najeriya. Wannan kanfanin ya saba dora alhakin wannan danyen aiki a kan masu tayar da kayar baya na wannan yanki, wadanda ake zargi da fasa bututun domin satar danyen mai. Sai dai Cikin wani rahoto da ta fitar a wannan alhamis kungiyar da ke da mazauninta a birnin London na Birtaniya, ta ce babu kamshin gaskiya a cikin wannan batu.

Darektan tsare-tsare na kungiyar AI da ke yaki da cin hanci da karbar rashawa a duniya Audrey Gaughran ta ce Shell na wadanda karayrayi ne domin kauce ma biyan diyan ga mazauna yankin Niger-Delta da suka shiga cikin halin ni 'yasu sakamakon matsalar malalar mai. kwararen kanfanin Accufacts na kasar Amirka da ya hada guywa da Amnesty International wajen gudanar da bincike ya nunar da cewa rashin amfani da bututun da ya dace ne ummal aba'isan malalar mai da gurbata muhalli a Niger-Delta.

Sai dai kuma cikin wanta sanarwa kanfanin hako mai na Shell ya mayar da martani inda ya yi watsi da Zargin marar hannu dumu-dumu wajen haddasa malamar mai a yankin Niger Delta. kanfanin ya nunar da cewa ya saba gudanar da bincike da kuma wallafa hotuna a shafinsa na Internet game da wannan batu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar