1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da muggan ayyuka a Agadez

January 4, 2022

Fataucin miyagun kwayoyi ya zama kalubale a birnin Agadez da ke Jamhuriyar Nijar, inda jihar ta zama wata hanya ta shige da ficen haramtattun kwayoyin.

https://p.dw.com/p/458ww
Symbolbild Kokain
Safarar miyagun kwayoyi na neman zama ruwan dare a AfirkaHoto: Orlando Barra/Agencia EFE/imago images

Ba dai fataucin miyagun kwayoyin ne kadai ke zaman kalubalen jihar da Agadez ba, har ma da fataucin mutane da kuma makamai, lamarin da ya sanya al'umma da jami'an tsaro suka tashi haikan wajen yaki da dabi'ar. A karshen makon da yagabata dai, jami'an 'yan sanda masu yaki da fataucin miyagun kwayoyi sun cafke hodar ibilis da nauyinta ya kai sama da kilo 200 da kudinta kuma ya kai Cefa biliyan biyar. Jami'an dai sun cafke hodar ibilis din ne a hanya Dirkou zuwa kasar Libiya, inda kungiyoyin fararen hula na Agadez nuna takaicinsu, ganin cewa a wannan karon har da wasu wakilan talakawa da aka kama dumu-dumu cikin wannan badakala. Kusan ko wannne lokaci jami'an tsaro na aiki tukuru, inda suke cin nasara kan masu fataucin miyagun kwayoyin. Matakin da jami'an ke dauka dai ya samu karbuwa wajen hukumomi da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi da ma sauran al'umma a  jihar ta Agadez, inda gwamnan jihar Elhadj Magagi Maman DADA ya jinjina musu tare da kira ga al'umma su bayar da goyon baya ga jami'an da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyin domin ganin bayan wanan matsala.