1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Dakatar da shari'a ga 'yan aware masu neman 'yanci

Zakari Sadou AMA
October 4, 2019

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya soke shari'ar 'yan awaren da ke son kafa kasarsu a yankin masu magana da Ingilishi a daidai lokacin ake dab da kawo karshen mahawara kan rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/3QkFb
Kamerun Zentral-Gefängnis in Bamenda
Hoto: picture-alliance/imageBROKER/R. Marscha

Wannan afuwar ta shugaban Kamaru Paul Biya ta samu karbuwa ga al'ummar kasar musamman wadanda suke yin gudun hijra domin ceton rayukansu duba da halin da suka tsinci kansu a ciki. Mutane 333 ne afuwar za ta shafa kana kuma hakan zai ba wa gwamnati damar cimma manufofinta na dinke barakar da ta kunno kai a yayin da ake dab da kammala babban taron koli na sulhu da tattauna rikicin da ke addabar Kamaru na 'yan aware da ya shafe tsawon shekaru uku. 

Al'ummar da ke bangaren masu amfani da harshe Ingilishi sun yi lale marhaban da wannan sassauci daya daga cikinsu shi ne sarkin Weh a karamar hukumar Fungom dake yankin Menchum a jihar Arewa maso yammacin Kamaru da ya yi gudun hijira zuwa Douala ya bayyana farin cikinsa yana mai cewa matakin abin yabawa ne.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Akalla mutane dubu uku suke rasa rayukansu wasu sama da dubu 500 biyar suka tsere daga gidajensu domin samun mafaka da rayuwa mai inganci daga sassan kasar dabam-daban kamar yadda kungiyar Crisis Group ta bayyana a baya, a yain da ake shirin kammala babban taron har yanzu 'yan adawa na ci gaba da nacewa a kan matsayinsu na sharadin cewa sai an saki shugabansu, Julius Ayuk Tabe da magoya bayansa da aka yi wa daurin rai da rai kafin su shiga taron.

Kawo yanzu dai ana jiran sakamakon abin da taron tattauna matsalolin Kamaru zai haifar duk da yake har yanzu da akwai wasu da suka kaurece wa muhawarar bisa zargin rashin gaskiya cikin taron, a yain da wasu masu adawa da taron mahawawar ke ci gaba da kafewa kan batun kawo sauyi ga kudin tsarin mulkin kasar, bukatar da ya kai ga firaminista cewa ba shine babban batun muhawarar ba.