Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 31.10.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Muhimmin abin da ya fi daukar hankalin jaridu da mujallun Jamus a wannan makon a cikin rahotannin da suka bayar dangane da nahiyar Afurka shi ne ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Joschka Fischer yake yi ga kasashen nahiyar tare da bayar da la'akari da bayanan da ya bayar lokacin da ya yada zango a Namibiya, kasar da ta taba wanzuwa karkashin mulkin mallakar Jamus. A lokacin da take gabatar da nata rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Jamus ta hakikance da alhakin dake kanta na mulkin mallaka ta kuma tsayar da shawarar kara karfafa taimakon da take ba wa Namibiya. A ziyara ta farko da ya kai a hukumance ga kasar da ta taba wanzuwa karkashin mulkin mallakar Jamus, ministan harkokin waje Joschka Fischer, ya ce akwai wani alhaki na musamman da ya rataya a wuyan kasarsa a dangantakarta da kasar Namibiya. To sai dai kuma duk da haka gwamnati a fadar mulki ta Berlin tana kan bakanta na cewar biyan diyya ba zai iya warkar da tabon ta'asar da 'yan mulkin mallaka suka tabka ba, kuma hakan na daya daga cikin dalilan da suka sanya Joschka Fischer ya ki ya fito fili ya nemi gafara a hukumance a game da ta'asar kisan kare dangin da Jamusawa suka yi wa 'yan kabilar Herero a fafutukarsu ta mamayar kasar Namibiyar."

A halin da ake ciki yanzun kasashen gamayyar tattalin arzikin yammacin Afurka Ecowas na shawarar tura sojoji zuwa Cote d'Ivoire domin sa ido akan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar a cewar jaridar Frankfurter Rundschau , inda ta ci gaba da bayanin cewar:

"Al'amuran sai dada rincabewa suke yi a kasar Cote d'Ivoire. Bisa ta bakin sakatare-janar na kungiyar Ecowas Muhammed Ibn Chambers shugabannin kasashen Ghana da Nijeriya na shawartawa a game da tura sojan kwantar da tarzoma domin katsalandan a rikicin. A wajejen karshen watan satumban da ya wuce ne 'yan tawaye suka janye daga gwamnatin wucin gadi da aka kafa sannan suka yi fatali da shawarar kwance damarar makamansu tare da zargin shugaba Laurent Gbagbo game da kin ba wa ministocinsu da aka nada cikakken ikon zartaswa da kuma hana musu ma'aikatar tsaro da aka yi musu alkawarinta. Yau kimanin watanni 12 ke nan da fara rikicin kasar ta Cote d'Ivoire, wacce ta rabu biyu bangaren arewaci dake hannun 'yan tawaye da kuma kudu dake karkashin ikon gwamnatin Gbagbo. Sojoji 3700 Faransa ta tura domin sa ido akan yarjejeniyar ta tsagaita wuta."

A can kasar Uganda yau kimanin shekaru 17 ke nan wata kungiya ta 'yan kirista dake kiran kanta wai Lord's Resistance Army (LRA) take muzanta wa mutane a arewacin kasar, kuma a yanzu lamarin ya dada kazancewa a cewar mujallar der Spiegel , wacce ta kara da cewar:

"Bisa ta bakin Bishop Charles Obaikol a yankin Soroti, 'yan tawayen ba yaki suke da gwamnati ba illa ta'asa kawai akan farar fula. A wasu #yan kwanakin da suka wuce dakarun kungiyar ta LRA sun tsare wata bus dake dauke da fasinjoji 22, wadanda suka yi musu yankar rago. Wannan ta'asar ta sanya dukkan mazauna Soroti suka amince da kirkiro sojan sa kai domin tinkarar 'yan tawayen, wadanda ke da sansanoninsu a kuryar arewacin Uganda suke kuma samun goyan baya daga gwamnatin Sudan a shekarun da suka wuce. Kasar ta Sudan ta dakatar da taimakonta ga 'yan tawayen ne bayan da kasar Amurka ta saka kungiyar LRA a cikin jerin kungiyoyin ta'adda a shekara ta 2001."

A ranar bakwai ga watan afrilun da ya gabata ne wani dan jarida mai suna Christian Liebig, wanda ke aiko wa mujallar Focus rahotanni, kaddara ta rutsa da shi a bakin aikinsa a kasar Iraki. Babban burin marigayin shi ne ya taimaka wajen ba da kafar samun ilimi domin kyautata makomar rayuwar jama'a a nahiyar Afurka. Kuma ko da shi ke bai cimma burinsa ba, mujallar tayi hadin kai da wasu kafofi domin kirkiro wata gidauniyar taimako da aka rada mata sunansa ta kuma gabatar da shirin taimako na farko wajen gina wata makaranta ta sakandare ga dalibai kimanin 500 a kasar Malawi. A lokacin da take bayani game da haka majallar ta Focus cewa tayi:

"A baya ga matsalar Aids dake addabar kasar Malawi, kimanin kashi 60% na al'umar kasar su miliyan 12 ba su san bihim ba. Wato ba su iya rubutu da karatu ba. A baya ga haka tana da dimbim marayu da aka kiyasce yawansu ya kai yara miliyan daya wadanda galibi iyayensu suka rasu daga cutar nan ta Aids, wacce aka ce kimanin kashi 50% na al'umar Malawin ne ke dauke da kwayoyinta."