Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Babban abin da ya fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan makon mai karewa dai shi ne kusantar junan da aka samu a kokarin da ake yi na sasanta rikicin kasar Sudan. A lokacin da take sharhi game da wannan ci gaba, wanda kuma take ganin har yau dai da sauran rina a kaba, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:
"A cikin kiftawa da Bisimilla ake fatan ganin wasu abokan gaba guda biyu sun sumbanci juna domin zama a karkashin wani yanayi na kawance da kwanciyar hankali da kuma raba dukkan albarkatu daidai wa daida tsakaninsu. Bayan yaki na tsawon shekaru 20, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane kimanin miliyan biyu ya kuma tagayyara wasu miliyan hudu a yanzu an cimma daidaituwa tsakanin gwamnati a birnin Khartoum da 'yan tawayen SPLA na kudancin Sudan a game da dakatar da gwagwarmayar da suke na dora hannu akan arzikin man fetur da Allah Ya fuwace wa kasar da daina kashe-kashe bisa dalilai na addini."
To sai dai kuma jaridar ta ce wannan yarjejeniyar, ko da yake tilas ne a yai madalla da ita, amma fa a daya bangaren tamkar an gudu ne ba a tsira ba. Jaridar sai ta kara da cewar:
"Duk da wannan ci gaba da aka samu tsakanin gwamnati a Khartoum da kungiyar SPLA a kudancin Sudan, amma fa har yau da sauran rina a kaba. Domin kuwa hatta a can kudancin Sudan akwai wasu kungiyoyin na tawaye dake adawa da dukkan gwamnati da kungiyar ta SPLA. Bugu da kari kuma tun misalin shekara daya da ta wuce ake fama da bata-kashi a yammacin kasar. A nan ma tsakanin 'yan tawaye ne da askarawan gwamnati."
Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau ta tofa albarkacin bakinta akan abin dake faruwa a lardin Darfur na yammacin Sudan inda take cewar:
"Kimanin mutane dubu uku suka yi asarar rayukansu sannan wasu dubu dari hudu kuma suka tagayyara tun bayan da aka gabatar da matakin tawayen a cikin watan fabarairun bara. To sai dai kuma ita kanta gwamnatin Sudan ce ummal'aba'isin wannan hali da aka shiga saboda tayi shekara da shekaru tana mai taimaka wa makiyaya da kudi da makamai tare da yin watsi da makomar sauran kabilun lardin na Darfur mai yawan mazauna miliyan bakwai."
A can makobtan kasashe na Habasha da Eritrea kuma tsofuwar gabar dake tsakaninsu ta fara yin tsamari, lamarin da zai iya sake jefa yankin cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Jaridar Die Tageszeitung tayi bitar lamarin ta kuma rawaito rahoton dake cewar:
"Ummal'aba'isin wannan sabon ci gaba dai shi ne kasancewar kasar Habasha, ko da shi ke ta cimma nasarar yakin da suka gwabza da Eritrea, amma ta kwashi kashinta a hannu a zauren shawarwarin sulhu. Domin kuwa wani kwamitin kasa da kasa da MDD ta nada daga bisani ya sake danka wa Eritrea wasu daga cikin yankunan da sassan biyu suke sabani kansu, wadanda kuma sojojin Habasha suka mamaye. A sakamakon haka aka kasa cimma daidaituwa akan zirin iyakar da za a shata tsakaninsu saboda adawar da Habasha take yi da wannan batu."
Daga can gabacin Afurka jaridar ta Die Tageszeitung ta zarce zuwa yammacin nahiyar domin nazarin halin da ake ciki a Cote d'Ivoire, inda bisa ga ra'ayinta ko da shi ke 'yan tawaye sun amince da shiga a dama da su a gwamnatin hadin gambizar kasar, amma fa akwai wani sabon rikicin da ka iya zama cikas ga hada-hadar zaman lafiyar wannan kasa ta yammacin Afurka. Domin kuwa shugaba Gbagbo na neman yin fatali da maganar garambawul ga siyasar kasar ta kuri'ar raba gardama. A karkashin yarjejeniyarsu ta sulhu dai ba a shigar da wata magana ta kuri'ar raba gardama ba ta la'akari da banbance-banbance na kabilun kasar da kuma kasancewar babu wani takamaiman matakin da aka gabatar don shimfida turbar zabe.