1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

July 22, 2004

Daya daga cikin matsalolin da masharhanta na jaridun Jamus suka tabo a wannan makon ita ce ta cin hanci da ta zama ruwan dare tsakanin jami'an gwamnatin shugaba Kibaki da aka nada misalin shekara daya da rabi da suka wuce

https://p.dw.com/p/Bvpo

Har ila halin da muke ciki yanzu rikicin lardin Darfur na kasar Sudan shi ne ya fi ci wa masharhanta na jaridun Jamus tuwo a kwarya, inda a wannan makon suka gabatar da rahotanni iri dabam-dabam a game da halin da yankin ke ciki. Misali jaridar Frankfurter Rundschau ta gabatar da wani dogon rahoto tana mai ambaton gargadin da ya fito daga bakin sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell a game da cewar Amurka ba zata saduda ga alkawururruka na fatar baki daga gwamnatin Sudan ba zata ci gaba da matsin lamba har sai gwamnatin ta dauki kwararan matakai domin kawo karshen mummunan halin da ake ciki a lardin Darfur. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a lardin Darfur yana barazana ne ga makomar mutane sama da miliyan daya kuma wajibi ne a kawo canjin lamarin tun kafin murna ta koma ciki. Abin lura a nan shi ne duk bukatar ke akwai na kara karfafa taimakon jinkai da kafofi na kasa da kasa ke gabatarwa, amma fa ita kanta gwamnatin Sudan ce ke da alhakin kawo karshen wannan ta’asa domin kare makomar lafiyar al’umarta."

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan halin da ake ciki a Sudan tare da ba da la’akari da zargin da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam ke wa fadar mulki ta Khartoum a game da hada kan dakarun dake keta haddin ‘yan Adam a lardin Darfur. Jaridar dai ta ci gaba ne da cewar:

"Wasu bayanai amintattu da suka fada hannun kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Rights Watch sun tabbatar da kiran da fadar mulki ta Khartoum ta gabatar ga jami’an tsaro dake lardin Darfur a game da taimaka wa dakarun Larabawa na Janjaweed da makamai. Wannan kira kamar yadda tarihin bayanan ya nunar, da farko an gabatar da shi ne a cikin watan fabarairun bara, sannan aka sake maimaita shi a cikin watan maris da ya wuce. Wani abin damuwa kuma shi ne kokarin da gwamnatin Sudan take yi na sanya wa dakarun na Janjaweed rigar sarki domin mayar da su dakarun ‘yan sanda ko na soja ta yadda zasu samu cikakkiyar dama ta cin karensu babu babbaka a lardin Darfur."

A can Afurka ta Kudu kamfanonin sarrafa motoci na fama da tafiyar hawaniya wajen gudanar da ayyukansu sakamakon wani yanayin da aka shiga na gwagwarmayar ma’aikata a cewar jaridar ciniki ta Handelsblatt ta kuma ci gaba da bayani da cewar:

"Gwamnatin Afurka Ta Kudu dai ta taka rawar gani wajen janyo hankalin kamfanonin kera motoci na kasashen ketare domin zuba jari a kasar tun bayan kifar da mulkin wariya. A karkashin dokokin da ta shimfida kamfanonin na iya shigo da kayan spare zuwa kasar ba tare da kwasta ba. Amma duk da haka kamfanonin na fama da wahala wajen tafiyar da ayyukansu, musamman ma sakamakon tashin da aka samu ga darajar takardun kudi na Rand da misalin kashi 60% idan an kwatanta da dalar Amurka ko kuma kashi 40% idan an kwatanta da takardun kudi na Euro, lamarin dake tsawwala tsadar farashin abubuwan da kamfanonin ke samarwa."

A can kasar Kenya ana zargin gwamnatin Mwai Kibaki da laifukan cin hanci daidai da tsofuwar gwamnatin shugaba Arap Moi. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Kimanin tsabar kudi na Euro miliyan 150 aka yi awon gaba da su daga baitul-malin kasar tun bayan da gwamnatin shugaba Mwai Kibaki ta kama ragamar mulkin Kenya misalin watanni 18 da suka wuce. A sakamakon matsalar cin hanci ‘yan kasuwa na ketare suka fara bijire wa kasar ta Kenya domin zuba jari a makobciyarta kasar Tanzaniya. Wasu ‘yan kasuwar ma nuni suka yi da cewar a karkashin sabuwar gwamnatin ta shugaba Kibaki yawan kudaden tsohiyar baki da suke bayarwa tuni ya zarce yawan abin da aka saba bayarwa a zamanin mulkin Arap Moi."