Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 24.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Zimbabwe na daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

A wannan makon mai karewa ma jaridun Jamus sun ba da rahotanni masu tarin yawa akan al’amuran nahiyar Afurka abin da ya hada har da ziyarar da shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya kammala a wasu kasashe na nahiyar makon da ya wuce. Mujallar FOCUS tayi amfani da wannan dama domin gabatar da rahoto akan wasu shirye-shiryen da shugaban na Jamus ya gane wa idanuwansa, wadanda kuma ko da yake sun zama tamkar zakaran gwajin dafi amma babu wani abin da suka tsinana wajen kawo canji ga mawuyacin halin da ake ciki a kasashen da lamarin ya shafa. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Dukkan jami’an taimakon raya kasar da shugaban Jamus Hiorst Köhler ya gana da su a kasar Habasha sun bayyanar masa a fili cewar har yau babu wani abin da aka tabuka domin shawo kan matsalar yunwar dake addabar jama’a a wannan kasa."

A wannan makon ne hukumarb zabe ta kasar Muzambik ta ba da sakamakon zaben kasar da aka gudanar misalin makonni uku da suka wuce, amma fa tsofuwar kungiyar tawaye ta Renamo ta ce ba ta amince da nasarar da jam’iyyar Frelimo dake mulkin kasar tun daga shekara ta 1975. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar sakamakon zaben tana mai cewar:

"Wani abin lura shi ne kasancewar da yawa daga cikin ‘yan kasar ta Muzambik sun dokata wajen ganin canji ya samu ga manufofin wannan kasa, shekaru 12 bayan kawo karshen yakin basasarta, amma duk da haka sai ga shi sun ba wa Armando Guebuza goyan baya. Akwai kuwa tababa a game da cewar yana da ikon kawo musu canjin da suke bukata akan manufa."

Har yau ana fama da ba ta kashi a tsakanin kabilun da ba sa ga maciji da juna a kasar Kongo su kuma dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD su kimanin dubu 10 da aka tsugunar sun kasa tabuka kome wajen dakatar da wannan fada. A lokacin da take rawaito rahoto game da haka jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Ainifin matsalolin da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Kongo Monuc a takaice suke fuskanta sun samo tushensu ne daga tsare-tsare da kuma dogon turanci na majalisar kanta da kuma su kansu sojojin kiyaye zaman lafiyar. Domin kuwa kusan dukkansu sun fito ne daga kasashe masu tasowa, wadanda ke sha’awar shigar da sojojinsu karkashin tutar MDD saboda yawan kudaden da suke kashewa akansu a cikin gida. Kazalika ba an tura su ne domin fada ba, a saboda haka tilas a saka ayar tambaya a game da abin da ya sanya MDDr take kashe abin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu daya a kowace shekara akan sojojin na Monuc."

Gwamnatin shugaba Mugabe na fama da kaka-nika-yi sakamakon adawar da shugaban yake fuskanta a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyarsa. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG har ila yau ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Duk da matsalolin da al’umar Zimbabwe ke fama da su, inda ake fuskantar hauhawar farashin kaya da karayar darajar takardun kasar da misalin kashi 600% da tabarbarewar kiwon lafiya da rashin guraben aiki ga jama’a, amma duk da haka ba su fid da kauna ba a game da cewar nan ba da dadewa ba mulkin shugaba Mugabe zai zo ga karshensa. Ba kuwa saboda yana da niyyar kakkabe hannuwansa daga al’amuran mulki ba, sai dai saboda gwagwarmayar kama madafun iko da ake fama da ita tsakanin jami’an gwamnatinsa. Domin da yawa daga mukarraban Mugabe da tsaffin dakarun yakin sunkurun kasar Zimbabwe sun fara dawowa daga rakiyarsa saboda ya kasa biya musu bukatunsu."