Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Matsalar yunwa a kasar Nijer na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi akansu dangane da nahiyar Afurka

A wannan makon ma daidai da makon da ya gabata, babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus shi ne bikin ranar matasa da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Kolon karkashin laimar Katolika, bikin dake samun halarcin Paparoma Benedikt na 16. To sai dai duk da haka Jaridun sun gabatar da rahotanni iya gwargwado dangane da al’Äamuran nahiyarmu ta Afurka, musamman ma matsalar yunwar dake addabar wasu sassa na yammacin nahiyar. A lokacin da take sharhi game da haka, jaridar DIE TAGESZEITUNG ta ba da misali da Nijer, inda take cewar:

“A baya ga mamayar da farin dango suka yi wa kasar Nijer da kuma rashin damina mai albarka, matsaloli na tattalin arziki na daya daga cikin musabbabin matsalar yunwar da ta rutsa da kasar. Domin kuwa kasar ba fama take yi da karancin abinci ba, illa kawai farashin kayan masarufin ne yayi tsada fiye da kima. Ita kanta gwamnatin kasar a wajejen karshen shekarar da ta gabata ta 2004 sai da ta kiyasce cewar kasar zata fuskanci gibin tan 200,000 na hatsi a wannan shekarar da muke ciki.

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG a cikin nata sharhin tayi kakkausan suka ne akan gwamnatin Nijer da sauran manazarta dake ikirarin cewar kasar bata fuskantar watza matsala ta yunwa. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Ire-iren wannan ikirarin akan fuskance shi a duk lokacin da wani yanki na Afurka ya shiga kaka-nika-yi da matsalar yunwa. An fuskanci hakan dangane da bala’in yunwar da ya rutsa da kasar Habasha a shekara ta 2000 kazalika a shekara ta 2003 lokacin da yankin kudancin Afurka ya fuskanci damina marar albarka. Ainifin matsalar dake akwai shi ne kasancewar kasashen da lamarin ya shafa, ba su da ikon ci da al’ummominsu ko da kuwa sun samu damina mai albarka, sakamakon bunkasar yawan jama’a da suke samu ba kakkautawa, inda kasar Nijer misali take samun bunkasar da ta zarce kashi 3% ga al’umarta. Muhimmin abin da zai taimaka domin dakatar da billar ire-iren wadannan matsaloli na yunwa shi ne nagartattun matakai na garambawul ga manufofin wadannan kasashe.”

A wannan makon aka gabatar da matakin farko na yakin neman zaben shugaban kasar Liberiya da za a gudanar nan gaba a wannan shekara, bayan shekaru 14 na yakin basasa da kasar tayi fama da shi. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Tun dai tafiya bata je nesa ba tsofon dan wasan kwallon kafar nan mai suna George Weah ya samu ci gaba, inda hukumar zabe ta kasar Liberiya ta sa kafa tayi fatali da karar da abokan takararsa suka daukaka na cewar wai George Weah yana amfani ne da takardun fasfo na kasashe biyu. Kimanin mutane miliyan daya da dubu 400 daga al’umar Liberiya su miliyan uku da dubu 600 suka yi rajista domin kada kuri’unsu a zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan oktoba mai zuwa. A baya ga George Weah, daga cikin masu shiga takarar zaben har da Ellen Sirleaf wacce ake sa ran zasu yi ja-in-ja da tsofon dan wasan kwallon kafar a wannan zabe.”

A yau ne kuma ake gudanar da zaben shugaban kasar Burundi, inda ko shakka babu za a tabbatar da Nkurunziza kan karagar shugabancin kasar ta tsakiyar Afurka, ganin cewar ba ya da wani abokin takarar da zai kalubalance shi, kamar yadda jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta rawaito ta kuma kara da cewar:

“Kasar Burundi sannu a hankali ta fara farfadowa daga barnar da yakin basasarta na tsawon shekaru 12 tsakanin Hutu masu rinjaye da Tutsi tsiraru, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane dubu 300. Wannan ci gaba da kasar ta samu a ‘yan shekarun baya-bayan nan ya zo ne sakamakon rawar gani da tsofon shugaba Piere Buyoya, dan kabilar Tutsi, ya taka wajen gabatar da matakin sulhu da dinke barakar dake tsakanin kabilun kasar guda biyu.