Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 21.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Kasar Faransa na shirin tura tankokin yakinta zuwa Cote D'Ivoire

Darfur

Darfur

Daga cikin batutuwan da suka shiga kannun rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka har da halin da ake ciki a Darfur da kuma sabon rikici a gabacin Kongo. Amma da farko zamu fara ne da wani rahoton da jaridar DIE TAGESZEITUNG ta rubuta a game da shirin da Faransa ke yi na tura tankokin yakinta zuwa filin daga a kasar Cote D’Ivoire. Jaridar ta ce:

“A daidai lokacin da ake kokarin gabatar da wani muhimmin mataki a kokarin sasanta rikicin kasar Cote d’Ivoire, kasar Faransa ke kokarin jan daga saboda yiwuwar shiga wani hali na ko-ta-kwana. Domin kuwa a karon farko a cikin tarihinta na katsalandan a Afurka kasar ta Faransa ta ba da sanarwa a game da shirinta na tura tankokin yaki na zamani samfurin AMX-10 domin rufa wa mayakanta da ta tsugunar a kasar Cote d’Ivoire baya. Tun a shekara ta 2002 Faransa ta tsugunar da dakarun soja dubu hudu a kasar domin shiga tsakanin sassan da ba sa ga maciji da juna. A cikin watan nuwamban bara an fuskanci arangama tsakanin sojojin Faransar da dakarun sa kai a Abidjan, inda mutane masu tarin yawa suka yi asarar rayukansu, kuma tun daga sannan ake kyamar sojojin da kuma rawar da Faransar ke takawa wajen sulhunta rikicin kasar ta yammacin Afurka.”

A kokarinta na kakkabe kashin kazar dake tattare da sunanta a kasar Cote d’Ivoire kasar ta Faransa a wannan makon ta dakatar da janar Henri Poncet, tsofon kwamandan askarawan nata dake Cote d’Ivoire bisa tuhumarsa da laifin kisan gilla akan wani dan kasar da aka dade ana nemansa ruwa a jallo bisa tuhumarsa da laifuka na fashi da makami da fyade da sauran miyagun laifuka. To ko Ya-Allah daukar irin wannan mataki zai iya sake dawo mata da martabarta a idanun al’umar Cote d’Ivoire? Lamarin dai da walakin, in ji jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG wadda ta ba da wannan rahoto.

Kazalika jaridar ta SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta gabatar da sharhi akan mawuyacin halin da har yau ake fama da shi a lardin Darfur dake yammacin kasar Sudan inda take cewar:

“Duk da matakai na taimakon jinkai da ake gabatarwa a lardin Darfur ba a samu wani sassauci ga radadin wahala da mazauna yankin ke fama da shi ba. A maimakon haka ma radadin nasu sai dada tsamari yake yi. Dubban daruruwan mutane suka yi asarar rayukansu a yayinda wasu miliyoyi kuma ke cikin hali na kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsu. Alhakin wannan mummunan ci gaba kuwa ba kawai ya rataya ne a wuyan fadar mulki ta Khartoum ba, wacce har yau take tattare da imanin cewar zata samu galaba kan ‘yan tawayen lardin da karfin hatsi, kazalika kafofi na kasa da kasa na da rabonsu na alhaki saboda gazawar da suka yi wajen shawo kan rikicin.”

Ita ma mujallar DER SPIEGEL ta bayyana irin wannan ra’ayi, amma sai ta dora wa Amurka alhakin lamarin, wadda ta ce a sakamakon sojoji dubu 150 da take da su a Iraki da kuma wasu dubu 18 a Afghanistan kasar ta Amurka ba ta sha’awar jin wata magana da ba da gudummawar soja domin kiyaye zaman lafiya a Afurka, saboda a ganinta ba ta da wata maslaha a wannan nahiya.

A can gabacin Kongo kuma al’amura sai dada rincabewa suke yi sakamakon farmaki da ‘yan tawaye na Hutu ke kaiwa yankin. A lokacin da take ba da rahoto akan haka jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Kimanin mutane dubu 10 suka tsere zuwa wani yanki dake kudu maso yammacin garin Butembo na lardin Kivu sakamakon farmaki da dakarun Hutu suka kai a wani yanki mai suna Kasuo ranar larabar da ta wuce. Wannan sabon hali da aka shiga ya haddasa sabani a fadar mulki ta Kinshasa.”