1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

December 16, 2005

Lambar yabo ta Zacharov da aka ba wa Hauwa Ibrahim na daya cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvQB

Da farko zamu fara ne da duba sharhin da jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta rubuta a game da lambar yabo ta Zacharov da aka mika wa lauyan nan ta Nijeriya Hauwa Ibrahim dangane da rawar da take takawa wajen kare ‘yancin mata. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Ita dai Hauwa Ibrahim lauya daga Nijeriya dake da shekaru 37 da haifuwa, ba wata ‘yar juyin-juya hali ba ce, manufarta shi ne ta wayar da kan jama’a game da wasu hukunce-hukuncen da aka zartar akan mata, wadanda suka yi daura da karantarwar addini da kare mutuncin dan-Adam. Wannan fafutuka tata ta haifar mata da bakin jini da kiyayya a tsakanin al’umar Nijeriya.”

Kasar Spain ta cimma yarjejeniya da kasashen Ghana da Mali a game da sake karbar bakin haure daga kasashen guda biyu dake kwarara zuwa harabarta. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar yarjejeniyar inda take cewar:

“A karkashin yarjejeniyar sake karbar bakin hauren kasar Spain tayi wa kasashen da lamarin ya shafa alkawarin ba su karin taimakon raya kasa. A lokaci guda kuma kasar Nijeriya, wadda tuntuni ake da yarjejeniyar sake karbar bakin haure tsakaninta da Spain tayi wa kasar ta Spain alkawarin sa baki domin taimakawa a shawarwarin da take gudanarwa tare da sauran kasashen Afurka dake bmakobtaka da ita.”

A karshen mako ne al’umar kasar Kongo mai fama da rikici zasu kada kuri’ar raba gardama akan wani sabon daftarin tsarin mulki a karo na farko tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta a shekara ta 1960. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta leka yankin na tsakiyar Afurka domin neman bayani akan yadda jama’a ke nakaltar wannan kuri’a, wacce ke da nufin dora kasar Kongo kan safifin tsarin mulki na demokradiyya da kawo karshen ta’asar ‘yan ta-kife. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“A hakika dukkan mutanen da aka nemi bayani daga gare su a game da sabon daftarin tsarin mulkin kasar Kongo su kan yi dari-dari wajen ba da amsa. Dalilin haka kuwa shi ne kasancewar jama’a ba su da wata masaniya a game da kuri’ar saboda ba wani takamaiman matakin da aka dauka na wayar musu da kai akan manufa. Gaba daya kofi dubu 500 ne na daftarin tsarin mulkin aka buga domin raba wa jama’a a kasar dake da mazauna miliyan 60. Masu alhakin shirya kuri’ar dai na ikirarin cewar wannan wata alama ce ta nasarar shawarwarin zaman lafiyar da aka gabatar, wadanda kuma suka kai ga kafa wata gwamnati ta hadin gambiza a tsakanin dukkan sassan da ba sa ga maciji da juna a yakin basasar kasar ta Kongo.”

A tsakiyar wannan makon ne mahukuntan Faransa suka kame janar Henri Poncet bayan fuskantarsa da tambayoyi da suka yi. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG dake ba da wannan rahoto ta ci gaba ne da cewar:

“Janar din kuma tsofon kwamandan rundunar kiyaye zaman lafiya a kasar Cote d’Ivoire, ana zarginsa ne da hannu dumu-dumu a kisan gillar da wasu sojojin Faransa suka yi wa wani dan kasar Cote d’Ivoire. Tun a cikin watan oktoban da ya wuce ne dai aka dauki wasu matakai na jan kunnen janar Henri Pocet bisa zarginsa da laifin kokarin kare sojojin da suka aikata wannan danyyen aiki, amma a yanzun sai ga shi gaskiya ta fito fili cewar shi ne ya ba da umarnin kisan, akalla, a fakaice.”