1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrin ya zama sabon fagen yaki a Siriya

February 21, 2018

Turkiyya ta yi gargadi da kakkausar murya dangane da abin da zai biyo bayan kutsawa gundumar Afrin da dakarun Siriya suka yi, domin taimaka wa mayakan Kurdawa da ke fafatawa da dakarun Turkiyyar.

https://p.dw.com/p/2t4nt
Syrien Konflikt in Afrin
Hoto: Getty Images/AFP/O. H. Kadour

Mayakan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin Siriya sun yi dandazo a birnin Afrin, suna rera wakokin yabo dauke da tutocin Siriya.

Tun a 'yan kwanakin baya ne aka hango isar wannan yanayi na arangama da juna tsakanin Turkiyya da Siriya kafin faruwarsa a zahiri.

Tun a ranar Litinin ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Cavusoglu ya yi gargadin cewar duk wani goyon bayan da Siriya za ta ba wa mayakan Kurdawan wadanda take kira 'yan ta'adda, zai samu mummunan martani daga bangarenta. 

Mevlüt Cavusoglu bai damu da Siriya da ta sa kai a wannan yakin a matsayin yankin na cikin kasar ba ne, musamman bayan nasarar da mayakan Turkiyyar suka samu a kan iyakokin Siriyar, wanda ya kara musu kwarin gwiwa na cigaba da kai farmaki.

Ga dai abin da kwamandan mayakan sa kai na Siriya da ke birnin na Afrin ke fadi.

"Mun zo cikin birnin Afrin ne domin tallafa wa 'yan uwanmu, kuma yanzu haka muna cikin tsakiyar yankin na Afrin gaba dayanmu, kuma za mu cigaba da fada a nan har sai mun ga bayan Turkawan da suka yi mana kakagida a cikin kasarmu."

Syrien Free Syrian Army Kämpfer in nahe Afrin
Mayakan kungiyar Free Syrian Army da ke samun goyon bayan Turkiyya a kusa da AfrinHoto: Reuters/K. Ashawi

A cewar shugaba Recep Tayip Erdogan na Turkiyya, suna wannan fada ne domin samar da yanayi mai kyau a wannan yankin ta yadda 'yan gudun hijira na Siriyar za su samu damar shigewa.

Sai dai abun da jawabin na Erdogan bai kunsa ba shi ne, gaskiyar cewar ba wai mutanen na tserewa daga Kurdawan ba ne, suna gudun hijira ne sakamakon gwabza fada a bangaren dakarun Siriya da sauran kungiyoyin ta'adda kamar su IS.

Goyon baya daga Rasha

Wani jami'in majalisar yankin na Afrin mai suna Suleiman Dchafar, ya bayyana cewar suna da labarun cewar Rasha ta ba wa Turkiyya izinin lalata komai a gundumar Afrin.

Bente Scheller ita ce shugabar gidauniyar Heinrich-Böll reshen birnin Beirut.

"Dangane da halin da ake ciki a Afrin wannan gaskiya ne, saboda Turkiyya ta fara wannan farmakin. Kurdawan na cikin hali na tsaka mai wuya, kuma ko shakka babu goyon bayan da suke da shi daga bangaren sauran Kurdawan da ke Siriya bai isa ba. Suna fuskantar hare-hare ta sararin samaniya daga Turkiyya. Don haka dole suka juya neman agajin gwamnati."

Deutschland Demo - Syrien Afrin - Konflikt Türkei-Kurden (Getty Images/J. McDougall)
Kurdawan Turkiyya a Jamus lokacin zanga-zangar adawa da matakin sojin da Turkiyya ke dauka a yankinHoto: AFP/Getty Images

Ayar tambaya a nan yanzu ita ce, me ya sa Mosko ta yi imanin cewar Turkiyya ce za ta iya yakar mayakan sa kai da ke kiran kansu na Jihadi fiye da Siriya?

Manazarta na ganin cewar Rasha dai na kokarin haddasa fada ne tsakanin membobin kungiyar tsaro ta NATO guda biyu wato Amirka da Turkiyya.

Wasu kuma na ganin cewar siyasa ce a bangaren shugaba Erdogan, duk da gazawar dakarun kasar, ya yi wannan jawabi ne don tabbatar wa al'ummar Turkiyyan cewar, fadan don su ne kuma suna samun galaba.

Turkiyya dai ta dauki kasadar shiga wannan fada gadan-gadan, ba tare da tunanin barazanar yaduwar yakin zuwa wasu yankunan kasar ta Siriya ba. A daya hannun kuma dangantakar da ke tsakanin Kurdawan Turkiyya da Siriya za ta kara karfi.

Ana iya cewar ita ma Mosko ba ta yi hangen nesa dangane da abin da rikicin zai haifar ba.