Afrika ta Kudu ta tura dakarunta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
January 6, 2013Talla
Fadar gwamnatin Afrika ta Kudun ce ta tabbatar da wannan labarin a wannan Lahadin inda ta ce gwamnatin shugaba Jacob Zuma ta dauki wannan matakin ne duba da yadda lamura na tsaro su ke cigaba da tabarbarewa a kasar.
Sanarwar har wa yau ta ce dakarun na Afrika ta Kudu za su bada gudumawa wajen ganin an raba 'yan tawaye da makaman da su ke dauke da su da kuma kokarin ganin an daidaita sahunsu inda za su shiga cikin sauran al'umma domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum kamar kowa.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu gabannin tattaunawa da za a yi tsakanin 'yan tawayen na Seleka da gwamnatin ta shugaba Francois Bozize.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu