Afirka ta Tsakiya: inda addini ya zama makamin yaki | Siyasa | DW | 20.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afirka ta Tsakiya: inda addini ya zama makamin yaki

A da Musulmi da Kirista suna zaman lafiya da juna a kasar. Amma yanzu wani yakin basasa ya barke tsakaninsu, wanda tushensa bai da alaka da addini.

Tun fil-azan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke matsayin wata kasa da aka manta da ita a tsakiyar nahiyar Afirka. Amma yanzu kasar ta shiga kanun labaru sabili da mummunan rikicin da ya kunno kai tsakanin Kiristoci da Musulmai, abin da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kwantata shi da kisan kare dangi da ya auku a kasar Ruwanda shekaru 20 da suka gabata. Duk da cewa kasar Faransa da kuma kungiyar AU sun tura dakaru amma sun kasa kawo karshen kisan bayin Allah da ake yi. Da alamu wannan rikicin ya zo wa duniya a ba-zata duk da cewa tun wasu watanni aka ga alamun barkewar yakin basasan.

Ndele ba ta da nisa, kalmar dake rubuce ke nan a gaban wani karamin shago dake unguwar Miskine mai cike da kantuna dake Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ana sayar da carbuna da Littafai kamar Alkurani mai girma a shagon. Sai dai Ndele sunan wani gari ne a arewacin kasar mai nisan kilomita 650 daga Bangui. Daga nan 'yan tawayen Seleka suka taso, wadanda a cikin watan Maris suka kwace bbirnin Bangui kana suka kifar da tsohuwar gwamnati.

Wata iyaka a cikin kasa

Unguwar Miskine kuwa ta kasance mazaunin Musulmi tsiraru a cikin mabiya darikar Katholika mafiya rinjaye a Bangui. A kewayen masallacin unguwar akwai coci guda uku. Gabanin juyin mulkin akwai kyakkaywan zaman lafiya tsakanin Musulman da Kiristocin. Amma yau wannan unguwa ta zama dandalin wani yakin basasa, inda 'yan bangar Kirista da Musulmi ke wa juna kisan gilla.

Ahmet Adam vor der Moschee

Ahmet Adam a gaban masallacin Miskine

Sai dai ba bambamcin addini ne musababbin wannan rikici ba, inji Ahmet Adam dan limamin masallacin Juma'a unguwar ta Miskine kuma kane ga daya daga cikin kwamandojin 'yan tawaye. Ga Ahmet Adam kam juyin mulkin ya halasta.

"Wannan ba rikici ne tsakanin Musulmi da Kirista ba. Mu dukka 'yan kasa guda ne. Rashin adalci shi ne dalilin juyin mulkin. A da ana daukar Musulmi a matsayin baki a babban birnin. Amma mu ma muna da 'yanci daidai da sauran 'yan kasa."

Musulmi ke da kashi 10 zuwa 15 cikin 100 na yawan al'umar kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Akasarinsu na zaune ne arewacin kasar inda ake rashin ababan ci-gaban kasa a cikin wannan kasa da a da ma ke fama da talauci. Babu makarantu, babu asibitoci babu hanyoyin mota. Kasancewa ana daukar kusan kwanaki 10 kafin a isa birnin Bangui daga arewacin kasar, mazauna wannan yanki sun fi karkata ga kasashen dake kusa da su wato kamar Sudan da Cadi. Asibitin garin Nyala dake cikin Sudan suke zuwa, sannan suna tura 'ya'yansu makarantun Islamiya a birnin Khartoum.

General Nouredim Adam

Janar Nouredin Adam, lokacin da yake rike da mukamin ministan cikin gida

Ko da ma dai akwai makeken gibi tsakanin arewaci inda Musuli ke da rinjaye da kudancin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda Kiristoci suka fi yawa, amma juyin mulkin da Seleka ta yi, ya kara fito da wannan bambamcin addini da al'adu fili. Yanzu haka dai Musulman ne ke rike da iko a birnin Bangui dake kudancin kasar. Dan uwar Adam, janar Nouredin Adam ya jagoranci wannan tawaye.

"Dalilin da ya sa muka jagoranci wannan tawaye a fili yake. Kasarmu na daya daga cikin kasashe da ba su da ci-gaba a duniya, duk da dinbim arzikin da Allah Ya huwace mata. Amma tsohon shugaban kasa Bozize bai tsinana wa Afirka ta Tsakiya komai ba. Ya gallaza wa al'umma. Ya sa an yi ta daure mutane ana kashe su. Bai da wata alkibla ga wannan kasa."

Sabbin hukumomi-sabbin mataloli

Sai dai karbe madafun iko da Seleka ta yi ya haddasa sabbin matsaloli. Mayakanta sun yi ta kwasar ganima. An kafa gwamnatin wucin gadi karkashin jagorancin Michel Djotodia, Musulmi na farko da ya taba darewa kan kujerar mulkin kasar. Sai dai gwamnatinsa ta rasa makama, an samu baraka tsakanin shugabannin Seleka, an kuma kori Janar Adam.

Tsohon shugaba Francois Bozize ya yi amfani da wannan damar, inda daga Kamaru inda yake gudun hijira ya hada kan 'yan bangar Kiristoci a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya don su farma 'yan tawayen Musulmi. Da ma dai ana jin haushin sabbin mahukuntan a Bangui.

Tsoffi da kuma sabbin shugabannin su yi amfani da mabiya addininsu a gwagwarmayar rike madafun iko. A karshe dai al'ummomin kasar ne gaba daya suka fi jin jiki.

Mawallafa: Simone Schlindwein / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin