Afirka ta Kudu:Taron shugabannin Afirka da Sin | Labarai | DW | 04.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu:Taron shugabannin Afirka da Sin

Taron da ke gudana a wata kasar Afirka a karon farko, zai yi nazarin dangantakar kasuwanci da wasu huldodi da ke tsakanin Sin da nahiyar ta Afirka.

Taron dai zai gudana ne a ranakkun Jumma'a da kuma Asabar inda ake sa ran shugaban kasar ta Sin Xi Jinping zai sanar da jerin wasu kwagiloli tsakanin kasarsa da kasashen na Afirka duk kuwa da cewa a baya-bayannan saka hannayen jarin da kasar ta Sin ke yi a Afirka ya ja da baya. A kalla dai shugabanni 40 ne na Afirka cikinsu har da Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya da kuma Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe za su hallara tare da shugaban na kasar Sin a birnin Johannesburg, na Afirka ta kudu.

Kasar da Sin da ke a matsayin abokiyar hulda ta farko ga kasashen na Afirka, na da ma'aikata fiye da miliyan daya da kuma kanfanoni fiye da 2000 da a halin yanzu ke cikin kasashen na Afirka.